AEDC, Kaduna DisCo sun zabtare farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin raba lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ya ba da sanarwar rage farashin wutar lantarkin da yake raba wa kostomominsa na runukunin Band A daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh.

A ranar Litinin AEDC ya bayyana haka saƙon dabya wallafa a shafinsa na X.

Sanarwar ta ce, “Muna farin cikin danar da rage farashin wuta ga kostomominmu na Band A, an yi ragin ne daga N225/kWh zuwa N206.80/kWh wanda ya fara aiki daga yau, 6 ga Mayu, 2024.”

Kamfanin ya kuma bai wa abokan mu’amalarsa na Band A ɗin tabbacin samun wutar lantarki na sa’o’i 20 zuwa 24 a kullum.

Sai dai, AEDC ya ce, “Farashin wutar na nan yadda yake ga kostomomin Band B, C, D da kuma E.”

A wata mai kama da wannan, shi ma kamfanin Kaduna Electricity Distribution Company, ya yi wa kostomominsa na Band A Albishi da zabtare farashin wutar zuwa N206.80/kWh daga N225.

Hukumar gudanarwar kamfanin, ita ce ta sanar da hakan a ranar Litinin.