Daga WAKILINMU
Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya sun yi taro tare da tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙarƙashin jagorancin mai kula da harkokin jinƙai, Mohamed Malick Fall, a Abuja ranar Juma’a.
Manufar taron dai ita ce neman tallafi don tunkarar babban ƙalubalen ci gaban yankin.
Taron wanda Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranta, ya samu halartar gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Kano, Mallam Umar Namadi na Jigawa; Mataimakin Gwamnan Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal.
Taron wanda aka gudanar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja, ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi matsalolin tsaro, da talauci, da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Gwamnonin sun kuma bayyana damuwarsu game da ƙaruwar shan miyagun ƙwayoyi, yawan mace-macen yara da mata masu juna biyu, da rashin aikin yi ga matasa.
Sun ƙara bayyana tasirin ƙalubale kamar gurɓacewar ƙasa da sauyin yanayi kan noma, wanda kusan kashi 80 na al’ummar ƙasar ke dogaro da su.
Bugu da ƙari, gwamnonin sun jaddada illar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ga ƙananan yara.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso-Yamma, ya jaddada buƙatar samar da tsarin haɗin kan yankin, inda ya ce, “Hanya ɗaya da za mu iya shawo kan ƙalubalen Arewa maso Yamma ita ce hanyar da ake bi a yankin da ke buƙatar mu haɗa kai ta hanyar haɗin gwiwa. Ya kamata mu haɗa karfi da ƙarfe wajen yaƙi da talauci da rashin aikin yi, kasancewar manyan su abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a yankin.”
Sai dai kuma Babban Jami’in Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya Mohamed Malick Fall, ya nuna farin cikinsa ga taron tare da tabbatar da aniyar Majalisar Ɗinkin Duniya na tallafa wa yankin na Arewa maso Yamma.
Ya bayyana muhimmancin rawar da yankin ke takawa wajen cimma muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs) a Nijeriya, wanda hakan zai amfani ɗaukacin nahiyar Afirka.
“Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar ganin ƙwaƙƙwaran jagoranci da jajircewar Gwamnonin Arewa maso Yamma na inganta rayuwar al’ummarsu. Za mu ci gaba da tallafa wa gwamnati da al’ummar Arewa maso Yammacin Nijeriya. Tare, za mu ceto da kuma hanzarta ajandar 2030 don ci gaba mai ɗorewa a yankin,” in ji Fall.
Fall ya ƙara sanar da gwamnonin game da yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta mayar da hankali wajen hanzarta cimma nasarar SDG ta fannoni shida: tsarin abinci, ilimi, kariyar zamantakewa da ayyukan yi, samar da makamashi, sauyin yanayi, da sauyi na dijital.
An kammala taron ne da yarjejeniyar samar da taswirar aiki, da tawagogin fasaha daga Majalisar Ɗinkin Duniya da na jihohi bakwai za su tsara, bisa tsarin tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya ga yankin.
