Baƙuwar cuta ta kashe mutane 13 a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Adadin mutanen da suka rasu sakamakon kamuwa da wata baƙuwar cuta ya ƙaru zuwa 13 a Jihar Zamfara.

Aqalla mutane 505, akasarinsu mata da ƙananan tara ne aka kai asibiti sakamakon kamuwa da cutar a ƙananan hukumomin Gusau, Maradun da kuma Shinkafi a jihar.

Haka zalika an samu ɓullar cutar a Jihar Sakkawato a ƙananan hukumomin Isa da Zurmi.

A watan Fabrairu aka fara samun ɓullar baƙuwar cutar a ƙauyen Tsibiri da ke Ƙaramar Hukumar Maradun.

Wani mazaunin Tsibiri ya ce daga lokacin “Zuwa ranar Lahadi 12 ga Mayu, 2024, mutane 228 ne suka kamu da cutar a ƙauyen.

“An kai wasu daga cikinsu Babbar Cibiyar Hana da yaɗuwar Cututtuka ta Shehu Shagari da ke Gusau, sabobda tsanin da abin nasu ya yi.

“Waɗanda nasu ke da sauƙi kuma an ba su magani an sallame su a Cibiyar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHC) da ke Tsibiri.

“A Shinkafi, a watan Afrilu aka fara samun ɓullar cutar kuma kawo yanzu ta kashe shida daga cikin mutane 100 da ta kai su PHC.

“Sama da 60 daga cikin mutanen da suka kamu a Shinkafi suna cikin mawuyacin hali, kuma an tura su zuwa Cibiyar Shehu Shagari,” in ji shi.

A cewarsa da alama cutar tana yaduwa zuwa makwabtansu don haka akwai buƙatar gwamnatocin jihohin biyu su ɗauki matakan dalike ta.

Kwamishinar lafiya ta Jihar Zamfara, Dokta Aisha Anka, ta ce alamomin bakuwar cutar sun hada da ciwon mara, zubar da yawu, kumburin hanta, zazzabi da jin kasala.

A cewarta, cutar na da alaka da shan gurbataccen ruwa kuma Cibiyar Shehu Shagari na aiki haikan domin gano musabbabin cutar da dabarun magance ta.

Kwamishinar ta ƙara da cewa tuni aka aika samfurin kwayar cutar zuwa ɗakunan gwaje-gwaje da ke Abuja da Legas domin gudanar da bincike.

By Editor