Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da fetur a ma’aikatun gwamnati

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da man fetur a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Nijeriya.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci motocin su koma amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas.

A jawabinsa ga Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, Shugaba Tinubu, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun komawa amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas a Nijeriya.

A cewarsa, hakan na daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ɗauka na tabbatar da wadataccen makamashi da kuma rage tsadarsa a ƙasar.

Ya kuma ba da umarnin soke duk takardun buƙatar sayen ababen hawa masu amfani da fetur da mambobin majalisar suka gabatar, yana mai umartar su da su je su mayar da takardun na neman sayen masu amfani da iskar gas.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa umarnin daga cikin matakan gwamnatinsa na tabbatar da amfani da makamashi mara gurbata muhalli, lura da cewa motoci masu amfani da iskar gas ba sa fitar da hayaƙi.

Hakazalika ya ce ababen hawa masu amfani da iskar gas sun fi sauƙin kuɗi, da yiwuwar sauƙin samu ga ’yan Nijeriya.

A kwanakin baya ne dai Ministan Kuɗi, Wale Edun ya yi rangadin masana’antar ƙera ababen hawa masu amfani da iskar waɗanda ya ce nan gaba kaɗan za a ƙaddamar da su domin amfanin ’yan Nijeriya.

By Editor