Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Juventus ta lashe kofin Italiya karo na 15, bayan da ta doke Atalanta da ci 1-0 a birnin Rome, a wasan da suka fafata ranar Laraba.
Ƙwallon ɗaya tilo da Dusan Vlahovic ya zura a mintina na huɗu da fara wasa ya tabbatar da nasarar Juventus, wanda ta lashe Kofin bayan shafe shekaru uku babu labari.
Tawagar Massimiliano Allegri da suka kawo matakin ƙarshe da nasara a wasanni uku kacal, sun nuna turjiya, tare da daƙile yunqurin Atalanta na lashe gasar.
Ɗan wasan gaban na Serbia ya sake cin wata amma aka soke ta saboda satar gida.
Ɗan wasan Atalanta da Nijeriya Ademola Lookman, da kuma Fabio Miretti sun buga ƙwallayen da suka bugo turke.
An bai wa kocin Juventus Massimiliano Allegri jan kati a ƙarshe-ƙarshen wasan saboda nuna rashin amincewa da wani hukunci. Shi ne kocin da ya lashe Coppa Italia biyar kuma mafiya yawa a tarihi.
Yunqurin Atalanta na lashe wani babban kofi ya ci tura bayan nasarar cin kofin Coppa Italiya tun shekarar 1963.
Sai dai suna da damar cin babban kofi a mako mai zuwa yayin da za su gwabza wasan qarshe na gasar Europa League da Bayer Leverkusen a birnin Dublin.
