‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Kaduna sun kashe mutum shida a wani hari da suka kai ƙauyen Ambe da ke yankin Ƙaramar Hukumar Sanga a jihar a ranar Lahadi da daddare.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan, tare da cewa an kama mutum guda da ake zargi da hannu a harin.

A cewar Hassan, bayan da ‘yan sandan yankin da rudunan Operation Safe Haven, daga suka tinkari mahara inda aka suka yi musayar wuta wanda a ƙarshe aka samu nasarar damƙe guda daga ‘yan bindigar sannan sauran suka tsere cikin daji ɗauke da raunukan alburushi.

Ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar mazaɓar Jema’a/Sanga, Daniel Amos, ya bayyana a sanarwar davya fitar cewa, mutum shida sun mutu sannan takwas sun jikkata sakamakon harin, wanda a halin yanzu ana ci gaba da yi musu magani a asibiti.

Amos ya yi tir da harin, tare da yin kira ga al’ummar yanki da a kwantar da hankula sannan a zauna lafiya da juna yayin da gwamnati ke ci gaba da lalubo mafita mai ɗorewa wajen magance matsalar tsaron da ta addabi yankin.