Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun sace manajan bankin a Zamfara

Daga BASHIR ISAH

Da tsakar daren Litinin wasu lyan bindiga suka yi dirar mikiya a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, sannan suka yi awon gaba da manajan Bankin Taj reshen Gusau Malam Mansur A. Kaura a gidansa da ke yankin.

MANHAJA ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare.

Majiyarmu ta ce haran sun kai harin ne ɗauke da muggan makamai, kuma sun yi harbe-harben bindiga don razanar da jama’a kafin daga bisani suka tinkari gidan manajan bankin suka yi gaba da shi.