Makamashi: Matsaloli da mafita a Nijeriya

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Kamar yadda mu ka kwana a makon jiya cewa, mafita daga dukkan tarin matsalolin da Nijeriya da ma wannan nahiya ta Afrika suke fuskanta ta fannoni daban-daban shi ne sauya tunani, daga gurvataccen tunani da ya ke dankwafar da kasar Nijeriya da nahiyar mu ta Afrika. Kai tsaye shugabannin na Nijeriya su sauya tunanin nasu na ɗaukar duk wata shawara da ta fito daga Yammacin Turai da uwar gijiyarsu Amurka.

Duk wata shawara da ta fito daga yammacin turai da Amurka tun bayan yakin duniya na biyu, shawarwarine na haɓaka qasashensu, misali cinikin makashin wuta man fetur da gas da kuma dangoginsu, cinikin ne na yaudara da zalinci sune kullum da riba, shiri ne na mai mayar da mai doki kuturu, wato dai kura da shan bugu gardi da karɓar kuɗi. Daga 1953 da aka gano man fetur a Nijeriya, waye yake amfana daga wannan arziki na ƙasa? Amsa yammacin turai da Amurka da wasu yan kalilan ‘yan Nijeriya.

Sauran ’yan ƙasa ribarsu daga wannan makamashi na man fetur shine talauci, fatara, hauhawar farashi a kasuwanni da kuma yunwa. Baya ga haka sai rika bin su a gonakinsu ko guraren da suke sana’arsu ta su, wato kamun kifi a na karkashe su, a kama na kamawa sai ambiya kuɗin fansa. Farko – farko amfara da fashi da makami, aka shiga rigingimun addini babu garin da ba a fafata da yaran Malam Mamman Marwa mai Tatsine ba, haka a Kudancin Nijeriya an fafata da ɗan fashi Anini da yaransa.

A wancan lokaci tattalin arzikin ƙasa ya taɓarɓare duk da cewa Nijeriya a kan gaba wajen fitar da ɗanyen makamashin man fetur da gas da kuma dangoginsa a Afrika ta uku a duniya, amma babu aikin yi ga mata da matasa, mutane sun zama mayunwata kamar yadda a ke ciki a yanzu, ba maganguna a asibitoci kuɗin da ake fita da su zuwa Turai da qasashen Larabawa da sunan neman lafiya ya ninka, wato ya zarta kuɗaɗen kasafin ƙasashen Afrika masu yawan gaske.

’Yan Nijeriya ba za su manta da ciwo bashin hukumar lamuni ta duniya (IMF) ba, da shirin nan na tada komaɗar tattalin arziki mai suna kowa yaji a jikinsa (SAP), da kuma hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje (SFEM). Cire tallafi ba sabon abu ba ne domin an tava cire tallafin kayan masarufi a ƙasar nan a wajajen shekara ta 1985. Rage darajar kuɗi shi ma ba sabon abu ba ne da kururuwar shaiɗan ta a buɗe iyaka, wato buɗe kasuwannin cikin gida da kayyaki daga waje, musamman abinci kamar yadda ake kiraye-kiraye a yanzu.

Dukkan waɗannan tsare-tsare yana zuwa ne daga shawarwari daga Turai da kuma Amurka ta hannun ’yan takarda (Elit) masu karɓar kamasho da la’ada don haka sai mun sauya tunani wajen karɓar ire-iren waɗannan shawawari. Bayan mun san sune tushen matsalolin da ake fuskanta sama da shekaru 70 kenan. Halin lahauwala na tattalin arziki, hauhawar farashin kayan masarufi, tsadar sufuri, wahalar wutar lantarki, rashin ruwan sha, duhun jahilci duk da jami’o’i da makarantun fasaha da dari (500) da suke yaye dalibai sama da dubu goma (10,000) a duk shekara. Amma sun zama jakuna da kayan litattafai a bayan su.

Matsalar Neja Delta da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa da yunƙurin kafa ƙasa Jamhuriyar Biyafra da ƙungiyar al’ummar Oduduwa (OPC) ta Yarabawa wadda ke yin kamfen ɗin a raba ƙasa, su yi tasu. Duk waɗannan su na zuwa saboda gurɓatacceen tunani da ya samo asali tun lokacin da aka yi wa Arewacin Nijeriya da na Kudu auren zobe a shekara ta 1914. Saboda haka sai an sauya tunani auren ya mutu, kuma ’ya’yan da aka haifa kowa ya zaɓi wa zai bi. Kuma a tambayi malamai magada Annabawa yaya za a yi da dukiyar da aka tara.

Tun da ’yan Nijeriya sun saba da kyauta, shugabanni sojoji da ’yan siyasa farar hula da su kansu Turawan mulkin mallaka sun koya wa ’yan Nijeriya ba su ilimi kyauta kuma dole, wanda gwamnan Kano na da, wanda yanzu shi ya ke riƙe da muƙamin shugaban Jam’iyar APC, wacce ludayinta yake kan dawo, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kwaikwaya, ‘Ilimi Kyauta Kuma Dole’, kamar yadda shi ya amfana ya kai shi har ya sami matsayin dakta a ilimin boko.

Saboda haka tunanin da za mu zo da shi shi ne man fetur da gas da kananzir na girki da wutar lantarki da ruwan sha su zaman kyauta ga ’yan ƙasa daidai buƙatarsa. Motocin sufuri su koma kyauta duk inda zaka a Nijeriya zaka hau motoci da sauran ababan hawa kamar jiragen ƙasa da na sama kyauta babu ko sisin kwabonka. Kamar yadda a wasu jahohi ’yan makaranta ba sa biyan kuɗin sufuri a Kano, haka ada jami’an tsaro (‘yan sanda, soja, jami’an shige da fice, da ‘yan kwastan da ma’aikatan gidan gyaran hali, DSS) dukkansu ba su biyan kuɗin sufuri. Akwai lokacin ma’aikatan NEPA ba su biyan kuɗin wata duk sai a dawo da su bisa doka.

A na fara wannan tsarin matatunmu na man fetur za su dawo suna aiki domin man fetur ya zama kyauta kamar yadda hasken rana ya ke kyauta, wato “solar energy” – makamashin zafin rana. Ga wani abin sha’awa iskar da mu ke shaqa (oxygen) domin mu rayu har yau ɗin nan kyauta mu ke shaqa a ƙasar nan duk da cewa masu ra’ayin jari hujja (capitalism) su na da ra’ayin a mayar da iskar ta ‘oxygen’ haja ta neman kuxi.

Masu wannan ra’ayi na mayar da komai kuɗi sun ce mutum yana yin numfashi sau 23,000 a kowacce rana, saboda haka idan zai rayu shekaru 60 zuwa 70, zai yi numfashi sau miliyan 600. Idan mutum zai shaƙi iska ta Dala ɗaya a kullum, ya na buƙatar Dala 360 a shekara, wato Naira 540,000 kenan. Saboda haka mutum da matarsa ɗaya da ’ya’ya uku yana buƙatar Nira Miliyan Biyu Da Dubu Ɗari Bakwai (2,700,000) a duk shekara, wanda wannan tsari yana tafe.

Za ka ji wannan zance kamar almara, amma shirye-shirye sun yi nisa, kamar yadda a ke ta ƙoƙarin tabbatar da tsare-tsaren ‘Artificial Intelligent’, inda mutum-mutumi zai riƙa ayyukan bil adama, shi kuma ɗan adam ya zama ɗan kallo. Zai haifar da rashin aikin ga mutane sama da biliyan uku. Albashinsu da kuma alawuns-alawuns ɗinsu tiriliyoyin daloli da zu koma hannun mutane ’yan ƙalilin, wato mutum 1,000 a duk faɗin duniya.

Wajibi ne a gare mu, mu sauya tunaninmu kafin su sauya mu daga masu gaskiya da amana da aiki tuƙuru da neman na kai da kuma rashin raina sana’a. Amma a hankali suka mayar da mu bautar kuɗi, babu mutunci illa kuɗinka har a ke yin kirari da ‘kuɗinka daidai shagalinka’, a na girmama ka yawan dukiyar kuɗinka shi zai ba ka sunan wani gini ko titi a garinku.

Makamashinmu shi ne karmo daga itacen yakuwa da itacen lalle da itacen kuɓewa da itacen auduga da itacen tafasa da kuma kara zube, karan da manoma ba su tare su guri guda ba sun yi bishiya da su shi ake kira kara zube da shi a ke yin makamashin kafin gawayi da kwal da kuma a yanzu man fetur da gas.

Tunda sun zama kuɗi, a sannu a hankali iskar da mu ke shaka za ta zama kuɗi, kamar yadda mu ka ambata a sama. Saboda haka lokaci ya yi na sauya tunani domin ka da a yi ma na sakiyar da babu ruwa.