Gwamna Abba ya rattaɓa hannu kan dokar tantance lafiya kafin aure a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son yin aure.

Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaƙa da su ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, ya ce samar da dokar ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sickle cell anemia HIV/AIDS, da hepatitis.

Wannan shiri dai ya yi daidai da ƙudurin Gwamnan jihar Kano na ingantawa da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya da nufin ganin Kano ta kuɓuta daga matsalolin kiwon lafiya.

Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure.

Har ila yau, dokar ta haramta duk wata wariya ko ƙyama ga mutanen da ke ɗauke da HIV/AIDS, sickle cell anemia, hepatitis da kuma wasu yanayi.

A ya yin rattaɓa hannun kan dokar, Gwamna Abba
Kabir Yusuf ya jaddada cewa manufar aiwatar da dokar ita ce, tabbatar da tsarkin aure a jihar Kano tare da tabbatar da haihuwar ‘ya’ya masu lafiya, ba tare da wata cuta da za a iya magance ta ba.

Bayan Majalisar Dokokin Jihar ta amince da amincewar gwamnan jihar Kano, an sanya hannu kan dokar a ranar 6 ga watan Mayun 2024, kuma za ta fara aiki daga ranar 13 ga Mayu, 2024.

Dokar ta ba da umurni cewa duk wanda ke da niyyar yin aure dole ne a yi gwajin cutar HIV, Hepatitis B da C, genotype da duk wani gwajin da ya dace kafin aure.

Bugu da ƙari, dokar ta haramta yin duk wata yarjejeniya ta aure ga mutanen da ke shirin yin aure ba tare da gabatar da takardar shaidar gwaji daga wata cibiyar lafiya da gwamnati ta amince da ita ba.

Kazalika, dokar ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin saɓa wa tanadin ta, ya aikata laifin da zai iya fuskantar tarar N500,000, ɗaurin shekar biyar, ko kuma duka biyun.