Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Jude Bellingham ya ci ƙwallonsa na 19 a wasan da Real Madrid ta lallasa Deportivo Alsves da ci 5 da nema a filin wasa na Santiago Bernabeu.
Ɗan wasan Ingila ɗin ne ya fara cin ƙwallo a wasan, wanda shine na farko tun da Real Madrid ta lashe kofin gasar La Liga ta Sifaniya.
Ƙwallon da Bellingham ya ci dai ta sa yanzu ya bai wa ɗan wasan gaba na Girona Artem Dovbyk tazarar maki guda a tseren da suke na lashe takalmin zinari, na wanda ya fi saka kowallo a raga.
Vinicius Jr ne ya ci wa Real Madrid ƙwallo ta biyu a minti na 27, bayan da Eduardo Camavinga ya saka masa wata ƙwallo a kusa da mai tsaron ragar Alaves.
Federico Valverde ya mayar da wasan 3-0 ana daf da tafiya hutun rabin lokaci, kafin daga bisani Vinicius ya ci ƙwallonsa ta biyu sakamakon wani ƙoƙari da ya yi na karan kansa.
Matashin ɗan wasa, Arda Guler, ɗan ƙasar Turkiya ya ci kwallo ta 5 a wasan, a cikin minti na 81.
