Wajibi ne matasa ku zama masu ƙwazo a Nijeriya – Barista Junaidu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kabo

An shawarci matasa maza da mata na Jihar Kano dama Nijariya bakiɗaya da su tashi tsaye wajen zama masu ƙwazo wajan neman halas domin kuwa ta haka ne matasa shugabannin gobe za su bada kyakkyawan musali ga sauran al’umma a wannan lokaci.

Wannan shawara ta fito ne daga baki shugaban gamayyar ƙungiyoyin ’yan kasuwa ta Singa da ake kira Singa Market Development Association Of Nigeria (SMDAN) Barista Junaidu Zakari, a lokacin da ya ke wajabi wajan walimar ɗaurin aure ’ya ga ɗaya daga cikin futattun ’yan kasuwar kano Alhaji Sani Asia, wanda aka gabatar a ranar Lahadi da ta gabata.

Haka kuma a ƙarshe ya bayyana cewa wajibi ne matasa su san addinin su, da al’adun sun a gari kuma su ɗau cewa aure ibada ne, akwai buƙatar yin haƙuri da ruƙon amana a tsakanin miji da mata wannan shi ne zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a gida ta yadda za a samu ’ya’ya masu tarbiyya da kishin al’umma da ƙasarsu wanda za su dama shugabanni nagari.

Kamar dai yadda shugaban ƙungiyar (SMDAN) ya bayyana a wajan wannan taro da ya samu halattar ɗimbin ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa, Malaman Addinin, Rarakuna, da sauran al’umma Kono da wajenta.

By Editor