Gudunmawar ’yan jarida ga inganta muhalli

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yau Juma’a 3 ga watan Mayu, ake bikin Ranar Kare ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya. Ana raya wannan rana ne, domin yabawa da irin faɗi tashin da manema labarai ke yi, a fagage daban-daban, don bayyanawa jama’a halin da duniya ke ciki, cikin gaskiya da ’yanci.

Har wa yau, ranar na kasancewa lokacin tunatar da masu faɗa a ji da gwamnatoci muhimmancin mutunta ’yancin ’yan jaridu, da kuma su kansu manema labarai a tuna musu haqqin da ke kansu na tsare gaskiya da adalci da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida a duk lokacin da suke bakin aiki.

Shekarar 2024 na daga cikin shekaru mafiya muni a tarihin ’yan jarida a duniya, sakamakon yadda ake cigaba da halaka manema labarai a yayin da suke bakin aiki don tattara ingantattun rahotanni da za a aika wa duniya game da abubuwan da ke faruwa a yankin Gaza, a dalilin luguden wutar da Isra’ila take yi wa Falasɗinawa mazauna yankin.

Wani rahoto da ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa-da-ƙasa, Reporters Without Borders, ta fitar an bayyana cewa, ’yan jarida kimanin 103 ne Isra’ila ta yi wa kisan gilla suna bakin aiki. A tsakanin watanni biyar da suka wuce, babu inda ba a kashe wani ɗan jarida ba.

An kashe su a ofis, a filin daga, a gidaje cikin iyalinsu, a sansanonin ’yan gudun Hijira, a asibitoci, da cikin motoci. Babu wani waje da za a ce ’yan jarida sun tsira daga kisan gillar azzalumar gwamnatin Isra’ila. A farko farkon mamayar da ta kai yankin Gaza, cikin watanni biyu na farko sai da aka hallaka wasu ’yan jarida 5 a Rafah.

Watanni uku na farkon wannan yaƙi da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinu, shi ne lokaci mafi muni a kashe-kashen da aka riƙa yi wa ’yan jarida. Kimanin kashi 80 cikin xari na kisan gillar da aka yi wa ’yan jarida 103 sun faru ne a tsakanin ranakun 7 ga watan Oktoba da 31 ga watan Disamba na 2023.

A wannan lokacin kusan a kowacce rana sai an kashe ɗan jarida ɗaya. An kashe jimillar ’yan jarida 26 a kwanaki 24 na watan Oktoba, ’yan jarida 28 a watan Nuwamba, 26 kuma cikin watan Disamba. A kowacce rana ’yan jarida na rayuwa ne cikin fargaba da tsoron abin da ka iya faruwa da su, sakamakon hare-haren jiragen yaƙi ko ta’addancin sojojin ƙasa, da ke yi wa fararen hula kisan wulaƙanci.

A baya, ƙasashe biyu da rayuwar ’yan jarida ta fi fuskantar barazana su ne Haiti da Mexico, inda rahotanni suka yi nuni da cewa kimanin ’yan jarida goma sha ɗaya ne aka kashe a shekarar 2022. In an ɗauke ƙasashen Syria da Ukraine da suka fuskanci yaƙin basasa a shekarun baya. Rayuwar ’yan jarida na cigaba da fuskantar matsaloli iri-iri, da ke haifar musu da tarnaqi wajen gudanar da ayyukansu.

Matsaloli irin na tsoma bakin gwamnatoci da ’yan siyasa wajen tilasta kafafen watsa labarai, ɓoye wasu bayanai, ko karkatar da gaskiya, ko hukunta waɗanda suka fallasa wani aikin rashin gaskiya ko almundahana da wasu jami’an gwamnati suke gudanarwa, yana sanya tsoro da rashin sakewa wajen aiwatar da aikinsu.

Tarihin aikin jarida a Nijeriya ba zai taɓa mantawa da madugun ’yan gwagwarmayar kare ’yancin ’yan jarida Ernest Ikoli, wanda sau uku yana bayyana rashin amincewarsa, cikin rubuce-rubucensa a jarida, don hana ƙasar Birtaniya aiwatar da shirinta na mayar da Nijeriya ƙarƙashin mulkin mallakar ƙasar Jamus a shekarar 1938.

Hakan ya nuna irin ƙarfi da tasirin da aikin jarida yake da shi tun a wancan lokacin, kodayake bayan samun ’yancin kai abubuwa da dama sun faru da suka jefa rayuwar ’yan jarida cikin haɗari, a wasu wuraren ma har da kisan gilla. Kamar abin da ya faru da Editan mujallar Newswatch, Dele Giwa.

Sashi na 39 sakin layi na 2, na Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa kowanne ɗan ƙasa ’yancin kafawa da gudanar da wata kafar watsa labarai, tare da bayyana ra’ayi ko fahimtarsa, ba tare da takura ba. Sai dai duk da haka wasu dokoki da gwamnati ke kafawa bisa wasu manufofi na tsaro ko yaƙi da cin hanci da rashawa, suna yi wa ’yan jarida dabaibayi wajen fitar da rahotanni kan haƙiƙanin yadda suke.

A bana, bikin ‘Ranar Kare ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya’ ya mayar da hankali ne wajen duba gudunmawar da manema labarai ke bayarwa wajen kare muhalli da binciken masana ilimin kimiyya kan ɗumanar yanayi da gurvacewar muhalli.

’Yan jarida na fuskantar ƙalubale masu yawa wajen nema da yaɗa muhimman bayanai da suka shafi gurvacewar muhalli, ɗumanar yanayi, dagwalon masana’antu, ƙauracewar dabbobi daga wani waje zuwa wani, saboda lalacewar muhalli, bushewar dazuka saboda sare itatuwa da sauran manyan dalilai masu nasaba da muhalli. Alhalin fitar da irin waɗannan bayanai na da tasiri ga tsare-tsaren gwamnatoci, da ingantuwar tsarin dimukraɗiyya.

Lallai ’yan jarida na buƙatar haɗin kan gwamnati da jami’an tsaro da sauran jama’a don samun sauqin gudanar da ayyukansu, da suka haɗa da bincike, tattara bayanai, hirarraki, da bankaɗo muhimman abubuwa da wasu ke ɓoyewa, da nufin ilimantar da jama’a da wayar musu da kai. Sannan kuma su fahimtar da gwamnati da masu ruwa da tsaki ƙalubalen da ke gabansu dangane da yadda za a inganta muhalli da rayuwar al’umma.

Kamar yadda taken bikin wannan rana ta bana yake nunawa, a kare haƙoƙin manema labarai da masana ilimin kimiyya don inganta muhalli, in an yi hakan babu shakka rayuwa za ta yi kyau, ilimi kan muhalli zai yaɗu, jama’a za su himmatu kan sauke nauyin da ke kansu na kula da muhallansu.

Abin farinciki ne yadda a ’yan watannin nan muke ganin wasu gwamnoni da muƙarrabansu da ƙungiyoyin jama’a suna ta dashen itatuwa, wanda hakan ke taimakawa a yaƙi kwararowar hamada, a samar da inuwa don magance tsananin zafin rana da ake fuskanta a wannan lokaci. Babu shakka sanin kanmu ne shuka bishiyoyi na da matuƙar amfani ga muhalli, musamman a irin wannan lokaci da duniya ke fuskantar matsalar ɗumamar yanayi da gurvacewar muhalli.

Lallai ne jama’a a karan kansu su kafa ƙungiyoyin yaƙi da gurɓacewar muhalli a yankunansu, su haɗa kai da ‘yan jaridu domin wayar da kan mutanensu musamman mazauna karkara, don a guji sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba.

A inda aka cire wata, sai a yi ƙoƙari a dasa wata a madadinta. A riƙa ziyartar tashoshin rediyo ana gabatar da shirye-shirye ko hirarraki game da gudunmawar da jama’a ke bayarwa a kan inganta muhalli, don zaburar da wasu da ke gida su ma su himmatu wajen kyautata muhalli.