DAGA MUKHTAR YAKUBU
Ƙungiyar DHS int’l& Project Rescue Nigeria Team ta yi nazari tare da binciko mutane 100 da suka yi fice wajen kawo cigaba tare da havvaka al’amuran da suka samar da bunƙasar Jihar Kano.
Binciken wanda ya hada kama daga malamai, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da sarakuna da masu fasaha da ƙungiyar ta gudanar a cikin al’ummar Jihar Kano domin duba da kuma zaƙulo mutanen da suka kawo cigaban Jihar Kano domin karrama su in da suka shafe tsawon lokaci suna gudanar da binciken.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne dai aka yi babban taro a Jami’ar Bayero inda aka yi bikin karramar in da al’umma daga ciki da wajen ƙasar nan suka halarta.
Taron mai taken ‘Kano 100 Heroes Award’ 2024 an sanar tare da karrama dukkan mutane 100 ɗin da suka cancanta a karrama. Cikin mutane 100 da suka samu wannan kambun akwai fitaccen mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala tare da kuma marubuci kuma jarumi Ado Ahamad Gidan Dabino.
Aminu Ladan Abubakar Ala dai an karrama shi ne a matsayin fitaccen mawaƙin da ya bayar da gudummawar sa ga Jihar Kano ta fuskar waƙoƙin hikima da faɗakarwa.
Yayin da shi kuma Ado Ahamad Gidan Dabino MON aka karrama shi a matsayin marubucin da ya bayar da tasa gudummawar ta fuskar rubuce rubuce domin cigaban Jihar Kano tsawon lokaci.
Da yake yi wa wakilinmu ƙarin bayani a game da fitowar sa cikin mutane 100 da aka karrama, Aminu Ladan Abubakar Ala ya nuna matuƙar farin cikin sa da samun wannan matsayi.
Domin a cewar sa “Abin farin ciki ne da na samu kaina a cikin mutane 100 da suka samu wannan kambu da karramawa don haka ina alfahari da wannan kyautar karramawa da na samu.”
Shi ma Ado Ahamad Gidan Dabino MON ya tabbatar da farin cikin sa da aka zaƙulo aka ba su wannan kyauta don haka abin alfahari ne a gare shi. Inji Ado Ahamad Gidan Dabino MON.