Rashin kyawun jirgi ya hana Shettima tafiya taro a Amurka

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ba zai samu halartar babban taron kasuwanci da ke gudana a Amurka ba sakamakon rashin kyawun Jirgin saman Shugaban Ƙasa.

Taron wanda haɗin gwiwa ne tsakanin Amurka da Afirka, an shirya Shettima zai halarta ne a madadin Shugaba Bola Tinubu, wanda zai gudana daga ran 6 zuwa 9 ga Mayu, 2024.

Sai dai kuma, ala tilas Shettima ya fasa wannan tafiyar saboda rashin kyawun jirgin da zai ɗauke su zuwa Amurka.

Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasar, Stanley Nkwocha, ya faɗa a ranar Litinin cewa, matsalar gyara da jirgin saman da zai ɗauki Shettima zuwa wajen taron ya fuskanta, ita ce ta hana tafiyar.

Nkwocha ya ƙara da cewa, Shettima ya yi na’am da shawarwrin masu kula da jirgin saboda ba shi da wani zaɓi.

Yanzu dai tun da mai aukuwa ta auku, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, shi ne aka ce zai wakilci Tinubu a wajen taron.

Daga cikin shugabannin Afirka da ake sa ran su halarci taron sun haɗa da Shugaba Joseph Boakai na Liberia da Shugaba Lazarus Chakwera na Malawi da Shugaba Joao Lourenço na Angola da Shugaba Mokgweetsi E.K. Masisi na Botswana da dai sauransu.