Gaza: An kashe mutum 34,789 an jikkata 78,204 – Shawesh

Daga BASHIR ISAH

Jakadan Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya ce kawo yanzu, adadin waɗanda aka kashe a Gaza ya ƙaru zuwa 34,789, sannan 78,204 sun jikkata.

Shawesh ya bayyana haka ne a wata sanarwar manema labarai da ofishinsa ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Mayu, 2024.

Sanarwar ta kuma taɓo batun manyan kaburburan da aka gano inda aka turbuɗe mutane dama, tari bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ta ƙara da cewa, abin da ake gani a yau, ba yaƙin Isra’ila da Hamas ba ne, amma yaƙin Isra’ila ne a kan Falasɗinawa.

Ta ci gaba da cewa da ma an san Isra’ila da irin wannan mummunar sana’ar ta kashe mutane. Don haka jakadan ya yi ga saura sassan duniya da kada su bari su zama ɓangare na farfagandar Isra’ila.

Sanarwar ta rawaito Babban Kwamishinan MƊD (UNHR) na cewa, “Mun kaɗu ainun game da manyan kaburburan da aka gano kwanan nan a zirin Gaza.

“An gano gawarwakin mutane sama da 390 a asibitocin Nasser da Al Shifa, da suka hada da mata da ƙananan yara, inda aka ce da yawa sun nuna alamun azabtarwa da yanke hukuncin kisa da yiwuwar binne mutanen da ransu.”