Fashin daji ya zama ‘harkar kasuwanci’ ga wasu jami’an tsaro da na gwamnati — Gwamnan Katsina

Daga BASHIR ISAH

Gwamman Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yi zargin akwai jami’an tsaro da na gwamnati da ke taimaka wa ‘yan fashin daji wanda a yanzu hakan ya za zama tamkar ”harkar kasuwanci” a gare su.

Dikko ya bayana haka ne a hirar da tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Juma’a.

Ya ce, “Yanzu lamarin ya zama sana’a. Harkar kasuwanci ta masu aikata manyan laifuka, wanda ake samun hannun wasu ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro a ciki.

“Wannan na daga cikin tarin dalilin dalilan suka sa har yanzu aka kasa ganin bayan ayyukan ‘yan fashin daji.”

A baya-bayan nan an ji yadda ɓarayin daji suka addabi sassan Arewacin ƙasar nan da hare-hare, musamman a ƙauyuka, inda suka kashe na kashewa sannan suka yi garkuwa da mutane da daman gaske.

Dikko ya ce, bai yarda cewa siyasa ce ummul aba’isin matsalar tsaron ƙasar ba kamar yadda wasu ke ra’ayi, maimakon haka ya danganta matsalar da talauci da rashin adalci.

Yana mai cewa, galibin matasa a yankin Arewa, da N500 ake jan ra’ayinsu su shiga harkar fashin daji.

A ƙoƙarin da suke yi na daƙile wannan matsalar ta rashin tsaro a jihohinsu, hakan ya sanya kwanan nan wasu gwamnonin Arewa suka niƙi gari suka tafi ƙasar Amurka domin lalubo mafita mai ɗorewa dangane da matsalar tsaron da ta addabi yankunnansu.