IKEDC ya rage farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Kamfanin Ikeja Electricity Distribution Company ya rage wa kostomominsa na rukunin Band A kuɗin wuta da za su biya zuwa N206.80 kan kowane kilowat a sa’a guda maimakon N225 da hukumar kula da lantarki, NERC a taƙaice ta amince da shi.

Mai magana da yawun IKEDC, Olufadeke Omo-Omorodion, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ragin kuɗin wutar zai fara aiki ne daga ranar Litinin, 6 ga Mayu, 2024.

Haka nan, ta ce a maimakon N225/Kwh da kostomominsu na Band A su biya bisa la’akari da ƙarin farashin da NERC ta yi, yanzu kamfanin ya rage musu farashin zuwa N206.80/Kwh.

Sai dai farashin kostomomin da ke rukunonin Band B, C, D, da kuma E, na nan yadda yake in ji sanarwar.

Matakin ragin ba ya rasa nasaba da kokawar da ƙungiyoyi da Kamfanonin suka da sauran jama’a suka yi tun bayan da NERC ta ba da sanarwar ƙarin kuɗin wutar.