Rashin ganin gwamna

Manhaja logo

Daga THALITHU ƘOƘI
 
Ni ba na ganin laifin masu ƙorafi a kan rashin samun ganin gwamna ko muƙarrabansa, magana ta gaskiya! Iya ra’ayinsu kenan bisa la’akari da abinda suke tsammani da suka rataya wa kansu da kuma yarjejeniyar zuci da suka ƙulla tsakaninsu da waɗanda suke ganin sun kama madafun iko a yanzu. Kamar ko yaushe, mu riƙa yi wa juna uzuri.

Na san mutane da dama a wannan Gwamnatin, sani na kut-da-kut, kuma mun dama sosai kafin a samu Gwamnati da su. Rashin ganinsu, ko rashin jinsu, ko rashin mu’amalantuwa da su a yanzu sam ba ya daga ni ya buga da ƙasa, saboda na sani a da nima na yi aiki a cikin gidan Gwamnatin nan da ake ta hayya hayya a kai, na kuma yi aiki kusa da wani Gwamna na Kanon a baya na san yadda matsutsan aikin suke, da kuma irin sammatsin da ke tare da aikin (Wasu abokaina a kan FB sun san haka). 

Mu’ammala da masu kujera ta siyasa na buƙatar dannewa kai ƙirji da kuma rage tsammaninsu, tare da kyautata musu zato duk kuwa irin zargin da kake a kansu.

Da dama mutane da-na-sani suka kuma san waɗanda suke kan kujeru a yanzu sun zo sun mun ƙorafin wasu sun daina ɗaukar wayarsu, kuma na ɗan yi amfani da dama tana ba su haƙuri kuma na yi nasarar haɗa su da waɗanda suke ƙorafi a kai abun ya wuce, su ma kuma abun mamaki, da zarar ka haɗa su da waɗanda suke ƙorafin akai sun samu ganawa da su sai ka ji sun yi shiru sun daina ɗaukar wayar ta ka kai ma. Ka ga abun ya zama irin abun nan na gwano ne da ba ya jin ƙanshin jikinsa.

Da dama su kan yi korafin ba a rama wa kura aniyarta ba a kansu musamman ganin irin gudunmawar da suka bayar. Zama lafiyan da na yi shi ne, ko aikin da na ke yi a yanzu bai daga ni ya buga da ƙasa ba saboda na san yadda Allah Ya shigar da ni cikinsa, haka zai fitar da ni in ya so, a lokacin da ya so ko ina so ko ba na so. Kuma haka ko wane aiki ya ke duk kuwa girmansa ko ƙawarsa.

Shi ɗan Adam, da ni da ku, da su duk wuyar gane hali ne da mu. In ba uzuri a rayuwa mu’amala wuya za ta yi.

Lokaci alƙali, kamar ko yaushe a ƙara haƙuri. Ga batun tsaro nan ya damalmale Arewa muna nan muna fafatawa a kan gani ko rashin ganin wani saboda Allah.
 
Ƙoƙi mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga Kano