Wai hukumar Hisba ta yi amfani da ƙarfi!

Daga DAKTA MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI
 
1) Wannan shi ne mafi girman rainin hankalin da ya jawo wannan babbar matsalar. Wai ana amfani da ƙarfi, kuma wannan maganar ta ruɗi ruɗaɗɗu, har ma da wasu masu hankalin. To yanzu sai ku je ku yi amfani da “banana” da “apple” da “carrot” da “honey” ku hana su, tun da ku ‘ya’yan masu amfani da daɗi ne. In ka ce ana amfani da qarfi, to sai ka faɗi yadda za a yi, in ba a yi amfani da ƙarfin ba.

2) Malam Sheikh Daurawa ya faɗa ya nanata cewa mutanen nan da ake ƙoƙarin saitawa a kan hanya, suna fitowa da makamai, to kawai ɗan Hisba sai ya tsaya a kashe shi, tun da shi jaki ne ko?

3) Sam bai kamata gwamna ya yi wannan maganar a wannan lokacin ba. Ka sani ba dole ba ne ya zamanto ka fi duk wanda yake cikin gwamnatinka iyawa da basira ba Wasu da yawa a gwamnatinka, sun fi ka fasaha, don haka ne ma ka ɗauko su ka ba su riƙo, kuma ba don ka fi su ba! 

4) Ko ɗan yaro ne in ya kangare sai an yi amfani da bulala, kuma addinin da Malam yake tutiya da shi, da dokar ƙasar da gwamna yake ganin an karya duk sun amince da haka. Balle waɗannan firɗa-firɗan tantiran balagaggun kangararrun ‘yan kwaltan! Waɗannan banzayen fasiƙan ne za a ce ana yi wa amfani da ƙarfi?

Yanzu don Allah me gwamna ya fi Sheikh Daurawa in ba mulki ba? Ta yaya za ka zo don ka ba shi aiki, kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa, don wasu maha’inta, wataƙila ma fasiqai, sun zo sun gaya maka ƙarya da gaskiya sai ka zo ka ce za ka yi wa Malamin da, da ma ba alfarma ka yi masa ba! Akwai wanda in ka ba shi Hisbah yanzu ka ɗaukaka shi, amma ba dai Sheikh Daurawa ba.

5) In ka ji irin wutar da Malam yake sha a wannan harkar ta Hisba, daga ciki da waje, sama da ƙasa, za ka sha mamaki. Amma maimakon in ma gyaran ne (kuma ni a ganina ba wani gyara) kawai sai ka zo, saboda kai ne gwamna? To ko ni, ba Sheikh Daurawa ba, ba zan lamunci wannan shiga hanci da ƙudundunen ba.

6) Kuskure dai an tafka shi. Muna fata kuma, Allah ya sa gwamnatin Abba ta gyara wannan babban ƙasurgumin kuskuren. Domin abin da zai biyo bayan kuskuren da kuma saukar Malam, abu ne da ya kamata a lura da shi a hankali. Don na ga wani bidiyo har wasu sun fara kai wa wasu ofisoshin Hisba hari. Ka ga lallai dole manya su zauna don a gyara wannan babban kuskuren da aka tafka. Muna tare da Malam!
 
Dakta Abdullahi malami ne masani kuma mai sharhi a kan al’amurra yau da kullum. Ya rubuto daga Beijing ta ƙasar Chana