Jerin wuraren da za a tantace masu neman aikin ɗan sanda

Daga BASHIR ISAH

Hukumar kula da shirin ɗaukar sabbin jami’an ’yan sanda ta fitar da jerin cibiyoyi guda 20 wanda a nan za a gudanar da shirin tantance masu neman aikin ɗan sanda a faɗin ƙasa.

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda (PSC) ce ta kafa wannan hukumar don taimaka mata wajen gudanar da shirin ɗaukar sabbin ƙananan jami’ai da ke gudana.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ‘Yan Sanda, Ikechukwu Ani, ya faɗa cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis cewa, yanzu ana kan matakin tantance lafiyar masu neman shiga aikin ne wanda zai ɗauki makonni biyu kafin kammalawa.

Ya ce duba lafiya shi ne matakin tantacewa na ƙarshe a shirin, kuma za a fara ne ya zuwa ranar 16 ga Afrilu, 2024.

Ga dai jerin wuraren da aka keɓe don gudanar da shirin tantancewar a faɗin ƙasa:

-Zone 1 Kano; Police cottage hospital Bompai, Kano
-Zone 2 Lagos; Police College Ikeja
-Zone 3 Yola, Police Clinic Yola
-Zone 4, Makurdi, Police Clinic Makurdi
-Zone 5 , Benin, Police Cottage hospital, Benin
-Zone 6, Calabar, Police hospital Calabar.
-Zone 7, Abuja, MD Abubakar Police Hospital Dei Dei Abuja
-Zone 8 Lokoja, Police Clinic, Lokoja
-Zone 9 , Umuahia, Police Hospital Umuahia
-Zone 10, Sokoto, PTS Clinic Sokoto
-Zone 11 Osogbo, Police Hospital Osogbo
-Zone12 Bauchi, PTS Clinic Bauchi
-Zone 13 Ukpo, Police Hospital Awka
-Zone 14, Katsina, Ibrahim Coomassie Cottage Hospital Katsina
-Zone 15 Maiduguri, Police College, Maiduguri
-Zone 16, yenagoa, Zone 16 Headquarters Yenagoa.
-Zone 17, Akure, Police Hospital Akure
-Zone 18, Yobe, Utral Modern Police Hospital, Gashua Road, Damaturu
-Zone 19, Kaduna, Police College Clinic Kaduna
-Zone 20, Gusau, Police Secondary School clinic Zaria Road Gusau