Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan daudu, Bobrisky ya faɗa a komar EFCC

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, ta tsare ɗan daudun nan, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky, bisa zargin wulaƙanta takardun kuɗi na Naira.

Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, shi ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an tsare Bobrisky ne ranar Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana a rukunin gidaje na Pinnock Estate da ke Legas bisa zargin watsa takardun Naira a wajen taro wanda hakan cin mutuncin kuɗin ƙasa ne