Mun haramta shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a Kano — El-mustapha

Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano ta ce dag yanzu ta haramta shirya fina-finai masu nuna faɗan ‘yan daba da harkokin ‘yan daudu a jihar.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami’in Yaɗa Labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman da kuma kwanan wata 3 ga Afrilun da ake ciki.

Sanarwar ta ce: “Biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da al’umma ke yi a kan shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu a jihar Kano, Shugaban Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, Abba El-mustapha, ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna faɗan daba da harkar daudu a faɗin jihar Kano.

“Abba El-mustapha na bada wannan umarni ne a yau jim kaɗan bayan wata ganawa da ya yi da manyan ma’aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan ‘yan masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood wanda suka haɗa da ƙungiyoyin MOPPAN, Arewa Films Makers, Daraktoci da kuma Furodusoshi.

“Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin ya ci karo da tarbiyya tare da al’adar al’ummar dake jihar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za a saka ido irin wannan gurɓatattun fina-finai su ci gaba da yaɗuwa a cikin al’umma.

“Abba El-mustapha ya gode wa ‘yan masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood dangane da haɗin Kai da kuma goyan bayan da suke bawa Hukumar a koda yaushe.

Ya kuma godewa al’ummar jihar Kano kan irin haɗin kan da suke bawa Hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saɓa da al’ada tare da tarbiyyar addinin Musulunci.

“Abba El-mustapha ya kuma yi alƙawarin ci gaba da barin ƙofarsa a buɗe domin karɓar shawarwari.

“A ƙarshe, ya bawa masu shirya irin wannan fina-finan damar wata ɗaya da su gyara ayyukan nasu kafin dokar ta fara aiki gadan-gadan a kan su,” in ji danarwar.