’Yan sanda sun cafke jigon kai harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce jami’anta sun kama wani Ibrahim Abdullahi, wanda aka fi sani da Mande, wanda ake kyautata zaton shi ne ya kitsa kai harin jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris ɗin 2022 da kuma yin garkuwa da ɗaliban Jami’ar Greenfield da kuma yawan sace-sacen da aka yi a Abuja.

An kama Mande tare da wasu da dama da ake zargi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a jihar Kaduna.

Yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan Kaduna a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Muyiwa Adejobi, ya ce an kama Mande ne bisa wasu sahihan bayanai da aka samu ta hanyar Abuja zuwa Kaduna ta hanyar Rido Junction a ƙaramar hukumar Chikun.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa na kasancewa shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma ya shiga cikin manyan ’yan bindiga kamar Dogo Gide da Bello Turji.

Rundunar ’yan sandan ta kuma bayyana cewa jami’an ’yan sanda sun kama wani fitaccen shugaban ƙungiyar masu garkuwa da mutane wanda ya kitsa harin da aka kai a cocin Katolika na Saint Raphael a watan Satumban 2023 a Fadan Kamatan inda aka ƙona wani limamin cocin ƙauyen ƙurmus.