’Yan ƙwadago sun buƙaci soke ƙarin kuɗin lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na Nijeriya, Joe Ajaero da Festus Osifo, yayin da su ke gabatar da jawabi na haɗin gwiwa a bikin ranar ma’aikata a Abuja, a ranar Laraba, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da soke ƙarin kuɗin wutar lantarki tare da sausauta duk wani nau’i na haraji ga al’umma.

A cikin buƙatu guda 18 da shugabannin ƙwadagon suka gabatar, sun ce ya kamata a sake duba aikin sayar da wutar lantarki a ƙasar don kar da a samu koma baya.

Bugu da ƙari, suna son gwamnati ta gaggauta fitar da motocin bas ɗin CNG a faɗin ƙasar kamar yadda aka amince.

Har ila yau, sun yi kira da a dakatar da duk wani nau’i na haraji da kuɗaɗen da gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi ke karba daga tattalin arzikin ƙasa na tsawon shekara ɗaya.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) a ranar 3 ga Afrilu, 2024 ta ƙara kuɗin wutar lantarki ga abokan hulɗar da ke cin gajiyar wutar lantarki na sa’o’i 20 a kullum. Abokan ciniki a cikin wannan rukunin an ce suna ƙarƙashin abin da ake kira da ‘Band A’.