An gano kaburbura ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu

Daga MAHDI M. MUH’D

Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa a rana ta 209 na ƙazamin yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al’ummar Palastinu, an gano kaburbura masu yawa a zirin Gaza.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abdullah Shawesh ya fitar ga manema labarai a Alhamis.

Sanarwar ta ce, “yaƙin ya bar kimanin tan miliyan 37 na tarkacen bama-bamai da suka fashe. An yi hasashen cewa za a ɗauki shekaru 14 kafin a kwashe ɓaraguzan da suak fashe ɗin.

“Ya zuwa ranar 1 ga watan Mayu, adadin shahidan Falasɗinawa ya kai 34,535, tare da raunata 77,704, baya ga dubban wasu da har yanzu ba a gano inda suke ba a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine ko kuma aka yi musu kamun tilas inda ake tsare da su a Isra’ila.

“Fursunonin Falasɗinawan suna fuskantar tsauraran matakai, suna samun abinci kaɗan kamar gutsure guda na burodi da ɗan ƙanƙanin abinci don kawai su cigaba da rayuwa da kuma hana su mutuwa, wanda ke haifar da ramewa da kuma mummunan sakamako na lafiya.

“Kusan mata masu juna biyu 155,000 suna kokawan samun abinci don tsira. Suna fama da yunwa da cututukan da suka dabaibaye su, a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin abinci da ruwa da kuma kula da lafiya, asibitocin haihuwa uku ne suka rage a zirin Gaza, kuma sun cika da majinyata. Likitoci da ungozoma suna sha da kyar don samar da isasshen kulawa ga jarirai.”

Ministan Sufuri na Falasɗinu Tariq Zourub ya bayyana cewa, asarar da aka yi a fannin sufuri a zirin Gaza ya zarce dala biliyan 3. Mamayar ta lalata kusan kilomita 945 na tituna da motoci 55,000, wanda ya yi daidai da kashi 65% na hanyoyin sadarwa da kuma kashi 60% na motocin da ke da lasisi a cikin tashar.

Kowace rana ana bayyana laifuffukan da Isra’ila ke yi a Gaza, kuma a kowace rana muna shaida wani sabon babi na laifukan kisan kiyashi.

Kwanan nan, an gano kaburbura da yawa a asibiyin Al-Shifa da na Nasser Medical Complex a yankin Zirin Gaza, wanda ke ɗauke da ɗaruruwan gawarwaki.