Masu zanga-zanga sun buƙaci a sake buɗe tuhumar N70bn da ake yi wa Matawalle

Daga BASHIR ISAH

Wasu masu zanga-zanga da suka mamaye harabar ofishin hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC da ke Abuja, sun buƙaci a sake buɗe ƙarar zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, na karkatar da kuɗaɗen jihar zuwa aljihunsa.

A ranar Juma’ar da ta gabata aka ga masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da saƙonnin buƙatar EFCC ta sake buɗe kes din badaƙalar almundahana a kan Matawalle.

Masu zanga-zangar sun nuna rashin gamsuwarsu kan yadda EFCC ke tafiyar da batun Matawalle, inda suka buƙaci hukumar ta ƙara himma sannan ta tabbatar da adalci.

Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na hukumar, Wilson Uwujaren, shi ne ya karɓi masu zanga-zangar a madadin Shugaban EFCC, Chairman Ola Olukoyede.

Uwujaren ya bai wa waɗanda lamarin ya shafa tabbacin hukumar ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ta bi diddigin zarge-zargen rashawa, tare da shan alwashin bin ƙwaƙƙwafin kowace ƙara a ƙarshe.

Kafin wannan lokaci, Bello Matawalle na fuskantar tuhuma ka wawashe sama da Naira biliyan 70 daga aljihun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna kamar yadda bincike EFCC ya bankaɗo.

Sai dai, tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Matawallen muƙamin ministan tsaro, sai aka ji shuru gane da ci gaban tuhumar.