Shin za a tsagaita wuta bayan kashe sama da Gazawa 34,000?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tambayar sanin yiwuwar tsagaita buɗe wuta da Isra’ila ke yi a Gaza na da muhimmanci don yadda a ke ta yunƙurin yiwuwar hakan amma sai a ke ta fuskantar cikas. Ba mamaki rashin niyyar Isra’ila ta dakatar da yaqin gabanin kashe duk ‘yan Hamas ke kawo kwan gaba kwan baya.

Tun mayar da martanin Isra’ila a sanadiyyar kutsawar mayaƙan Hamas cikin Isra’ila ranar 7 ga Oktobar bara a ke ta samun labaru masu ban takaici na yanda hare-haren Isra’ila ke yawan kashe mata da ƙananan yara. Ko yanzu ai Isra’ila ta wuce ramuwar gaiya ga Hamas don dubban Falasɗinawa da ta kashe kuma ta ke cigaba da kashewa.

Ran Balasɗine ba wani daraja ya ke da shi a idon Isra’ila ba. Duniya kan fi nuna dimaucewa in an taba Bayahude ko da kuwa kashe Falasɗinawa ne aikin sa ko aƙidarsa. Ba wata tambaya da a ke yi kan sanadiyyar harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila sai batun murƙushe Hamas da aiyana ta a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda.

Ma’ana ba a duba irin gallazawar da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa dare da rana da ta sa mayaƙan na Hamas shirya farmaki. Haƙiƙa Hamas ba baƙuwar kisa ba ce daga Isra’ila don yadda Isra’ila ta riƙa farautar shugabannin Hamas ta na kashewa. Shi kan sa shugaban Hamas na yanzu Isma’il Haniyeh na da nisan kwana ne don Isra’ila ta harba makamai da za su daidaita naman sa amma Allah ya sa da sauran shan ruwan sa.

Duk da haka a kwanaki ma Isra’ila ta kai hari ta kashe ‘ya’ya da jikokin Haniyeh a Gaza. Ba wata ƙasar yamma kai ba na ganin ko Larabawa sun jajanta kisan ko yin ta’aziyya ga Haniyeh. Dalilin a fili ya ke duniya na bin muradun yammacin duniya da ke ɗaukar Haniyeh a matsayin jagoran ƙungiyar ‘yan ta’adda maimakon aikin gwagwarmayar ceton yankin Falasɗinu daga mamayar Yahudawa da ya fara tun 1948.

Yau in da za a kai hari a kashe Haniyeh ba abun da za a ce illa an rage mai yiwa Isra’ila tawaye. Gaskiya ɗaya ce in za a bita a ba wa Falasɗinawa ‘yancin su. Isra’ila ta fice daga yankunan Falasɗinawa da ta mamaye ta bar su su more kasa mai ’yanci. Ko da wasa Isra’ila ba ta sha’awar ganin Falasɗinawa sun mallaki qasar su don haka duk wanda ya yunƙuro don karfafa neman ‘yanci zai iya samun kan sa a lahira ko gidan yarin Isra’ila.

Wanda ta zo ma sa da sauƙi ya zama ɗan gudun hijirar dole a wasu ƙasashe ƙalilan da kan iya karɓar baƙuncin Falasɗinawa. A takaice wasu ‘yan Hamas da ke ƙetare ba sa tsira daga kisan Isra’ila. A zahiri in mutum ya na Hamas to kafarsa ɗaya ta na duniya daya ta na lahira.

Jinjinawa Falasɗinawa masu gwagwarmayar kwatar ‘yanci da za a yi ita ce ba sa firgita don harin da zai kai ga kashe su. Ba ‘yan Hamas kaɗai ba hatta masu ƙoƙarin ɗauko labarun yanda Isra’ila ke gallazawa Falasɗinawa ba su tsira ba. Ba mu manta da yanda wani jami’in tsaron Isra’ila ya auna wakiliyar gidan talabijin na Aljazeera Shireen Abu Akleh ya harbe ta har lahira lokacin da ta ke aikin ɗaukar labaru a wani sansanin ‘yan gudun hijira na Falasɗinawa.

Kisan Shireen ya zama abun mamaki don ta na sanye da falmara mai ɗauke da alamar kasancewar ta ‘yan jarida baro-baro wato PRESS. Har yanzu ba a bi kadun jinin Shireen ba don ai Isra’ila ce ‘yar lelen manyan duniya ta kashe ta. Mu ƙaddara Hamas ce ta kashe ‘yar jarida Bayahudiya ai kuwa wannan ran ɗaya ba mamaki sai ya sa Isra’ila kashe ɗaruruwan Falasɗinawa kuma maganar ba za ta taɓa mutuwa ba don zai yiwu a ware wata rana ta tunawa da hakan. Amma Shireen sai shiru banza ta ci!

A nan ya na da muhimmanci duniya ta maida hankali wajen samun ‘yanci fiye da raba kai tsakanin masu marawa Isra’ila baya da masu tausayawa Falasɗinawa. Isra’ila kan iya biris da qudurin majalisar ɗinkin duniya kuma ba ta fuskantar ko da Allah wadai ne don ta fake ne da cewa ta na kare kan ta ne alhali ta jefa ‘yancin miliyoyin Falasɗinawa a garari. Shin su Falasdinawa ba ‘yan Adam ba ne ko kuma kwatar ƙasa su ka yi daga wajen wata ƙasar? Ai rashin adalcin ma a fili ya ke kamar hasken rana. A daki mutum a hana shi kuka kenan. Ga mari ga tsinka jaka.

A gefe guda yadda fadar Ramallah ke juyawa tsarin Hamas baya da gwale irin muradun ƙungiyar na ba wa Isra’ila kwarin gwiwar cigaba da gallazawa Falasɗinawa.
Masar ta tura tawaga Isra’ila don zantawa kan cimma tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da HAMAS.

Masar da ke maƙwabtaka na son ƙarfafa batun tsagaita wuta dokimiyyar kawo tallafi ga al’ummar Gaza.

Wannnan na zuwa daidai lokacin da Isra’ila ke dagewa sai ta kai farmaki ta ƙasa a Rafah da ke kudancin Gaza kan iyaka da Masar.
Wani jami’i ya ruwaito shugaban hukumar sirrin Masar Kamel Abbas na nuna Masar ba za ta bar Isra’ila ta jibge sojoji a kan iyakar ta ba.

Gwamnatin Isra’ila ta ƙara jaddada muradin kai farmakin ƙasa zuwa garin Rafah na kudancin Gaza.

Wani jami’in gwamnatin Isra’ila ya tabbatar da wannan shirin da ya haɗa da abun da Isra’ila ke faɗa cewa za ta kwashe fararen hula daga Rafah don kai hari kan ‘yan HAMAS.

Isra’ila ta ce ta sayo tantuna dubu 40 da kowanne zai iya ɗaukar mutum 10-12 don jama’ar da za ta kwashe.

Aikin kwashe mutanen zai kai wata ɗaya inda ya nuna daga nan sojojin Isra’ila za su ƙona Rafah.

Isra’ila dai a nan ta yi biris da kiraye-kirayen ƙasashen duniya da majalisar ɗinkin duniya na illar kai farmakin kasa kan Rafah da ke zama mafaka ga akasarin Falasɗinawa da su ka yiwo gudun hijira daga arewacin Gaza.

Hamas ta ce ta samu amsar Isra’ila kan shirin tsagaita wuta a yaƙin Gaza da a ke neman cimmawa.

Wannan ya biyo bayan yunqurin Masar da Katar da ke shiga tsakanin sassan biyu.

Duk da ba wani sabon abu daga vangaren Isra’ila , Hamas ta ce za ta nazarci matsayar ta musayar kamammu da Falasɗinawa da ke kulle a gidajen yarin Isra’ila.

Mai ba da shawara kan tsaro na fadar White House Jake Sullivan ya ce ya ga alamun za a samu nasarar cimma yarjejeniyar dakatar da yaƙin.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 34,000 a yankin Gaza mafi akasari mata da ƙananan yara.

HAMAS mai mulkin Gaza ta tura wakilai Masar don tattaunawa kan matsayar Isra’ila a sabon shirin tsagaita wuta.

Wakilan Masar sun ziyarci Isra’ila kan shirin tsagaita wutar da togaciya ga Isra’ila kar ta shigo Rafah da zai iya saka ta jibge sojoji kan iyakar Masar.

Tawagar HAMAS zuwa Masar na ƙarƙashin jami’in ta Khalid Al-Hayya.

Masar da Katar na aiki don ganin tsagaita wutar da ya gagara tun bara inda a ka dakatar da yaƙi na tsawon mako ɗaya.

A tsagaita wutar ta baya Isra’ila ta sako fursunonin Falasdinawa 270 inda ta samu karɓar mutanen 80 da ke hannun HAMAS.

Za a jira ganin yiwuwar sabuwar yarjejeniyar don samawa al’ummar Gaza sauƙi da kaucewa aukawa Rafah.

Saudiyya ta ce kafa ƙasar Falasɗinawa mai ‘yanci a gefe da ta Isra’ila ne hanya sahihiya ta hana maimaituwar fitina.

Wannan dai za a iya cewa ita ce matsayar akasarin ƙasashen Larabawa.

Ministan wajen Saudiyya Faisal bin Farhan ya ce tsayawa da gaske kan kafa ƙasar Falasɗinu a gefe da ta Isra’ila ne zai hana yawan dawowar fitinar Gaza.

Farhan ya ce su a yankin ba wai kawai za su tsaya kan yayyafawa wutar fitina ruwa ba ne amma har da daukar gagarumin matakin kafa ƙasar Falasɗinawa da hakan ne maslaha.

Hakan inji Farhan zai zama rigakafin dakatar da dawowar fitina a shekara 3 ko hudu kamar yadda kenan a ke fama yanzu.
Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken ya gana da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu don matsa qaimi wajen samun nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Gaza.

Blinken ya yi ganawar ta tsawon sa’a biyu da rabi a birnin Ƙudus.

A nan ya nuna Amurka na nuna matsa lamba kan Isra’ila kar ta yi kafar angulu ga shirin na tsagaita wuta.

Shirin dai da Masar ta jagoranta ya qunshi sako mutum 33 da kasar Isra’ila da ke hannun Hamas inda ita kuma Isra’ila za ta sako fursunoni Falasɗinawa da dama da ke gidajen yarin ta.

Amurka dai ce babbar kawar Isra’ila da ke sama ma ta makamai da duk wani ɗauki amma duk da haka ba ta yin gwanin ta ga duk lokacin da ta nemawa Falasɗinawa wani sassauci.

Kammalawa;

Netanyahu duk da yadda ya ke da tsauri kan neman murƙushe Hamas da haramar afkawa Gaza; amma akwai ‘yan jam’iyyar kare aqidar Yahudawa da ya haɗa kawancen kafa gwamnati da su da ke matsa ma sa lamba lalle sai ya yi biris da kiraye-kirayen duniya kan takatsantsan da afkawa Rafah.

In za a tuna hatta kauda ido wajen kaɗa ƙuri’ar neman dakatar da hare-hare da tabbatar da ba da agaji ga al’ummar Gaza da Amurka ta yi a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya ya fusata Netanyahu har ya furta kalaman rashin godiya ga Amurka. Tamkar dai wajibi ne Amurka ta yi wa Isra’ila abun da take so ko da hakan zai ja wa Amurka baƙin jini a sauran ƙasashen duniya.

Wannan ma a fili ya ke tun da Amurka ta shiga sahun masu kira ga Isra’ila da sam kar ta tura sojojin ƙasa cikin Rafah don asarar rayuka da hakan zai haddasa amma Netanyahu ya kekasa kasa ya ce sai ya kai harin don hakan ne cimma burin Isra’ila na shafe Hamas daga doron ƙasa.

Hakanan sam Isra’ila ba ta son jin batun neman ƙafa ƙasar Falasɗinawa don manufar al’ummar Falasɗinu su cigaba da zama tamkar bayi a hannun Isra’ila. In dai Falasɗinawa za su biyewa jagorancin gwamnatin su ta jam’iyyar Fatah da ke birnin Ramallah to haka za su iya dauwama a tattaunawa marar qarshe da fuskantar kisan ɗauki dai-dai gami da tura musamman matasan Falasɗinawa masu ƙin jinin mamaya gidajen yarin Isra’ila.

Ya na da muhimmanci ƙasashen Larabawa su tsayawa Falasdinawa don taimakawa gwagwarmayar ‘yancin ƙasar su daga Isra’ila mai samun dukkan goyon bayan da ba sharaɗi daga yammacin duniya.