KNEP da AFAN za su tallafa wa manona da takin a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Ƙungiyar manoma a Jihar Jigawa mai Suna Kenap ƙarƙashin jagorancin Alh Nura Ahmed Sale, ta ce za su haɗin gwiwa da ƙungiyar AFAN wajen samar wa anoma taki mai inganci cikin sauki a Jihar jigawa .

Sale ya buƙaci haɗin kan ƙungiyar Afan ne saboda karfinta da kuma yadda take taimakon manoma a Nijeriya.

Ya ce haɗinkansu ya zama dole domin saida haɗakai ne za su iya cimma burinsu na nuna wa manoma yadda ake amfani da wannan takin mai cokali.

Ya ce takin na da inganci fiye da buhun takin zamani mai nauyin 25kg, kuma in ka zuba cokali ɗaya na takin zai maka goyo biyu na goran feshin magani.

Da yake bayyana alfanun takin ga manoma, jami’in ya ce takin yana d’ɗauke da sinadari mai yawa da manoma suke buƙata don bunƙasa harkikinsu na noma.

A nasa ɓangaren, Shugaban ƙungiyar AFAAN, Alh Idris Ya’u Mai Unguwa ya ce, takin yana da ƙarfi kuma zai taimaka wa manoma wajen inganta noma a Nijeriya.