Tudun Biri: Sojoji 12 sun gurfana gaban kotunsu bayan kammala bincike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, ta kammala binciken da aka daɗe ana dakon sakamakonsa kan bom ɗin da aka jefa bisa kuskure kan mutanen ƙauyen Tudun Biri a Ƙaramar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.

Ta kuma ce, sojojin da aka samu da laifi a kai harin, za su gurfana a gaban kotun soji, domin fuskantar hukunci.

Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron Nijeriya, Edward Buba, ne ya bayyana haka a taron manema labaran da aka gudanar a Abuja.

A Disambar bara ne wani jirgin sojoji ya jefa bom kan mutanen da ke bikin Maulidi, lamarin da ya janyo asarar rayuka da jikkatar wasu da dama.

Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki alhakin kai harin, inda kuma ta ce, lamarin ya faru ne bisa kuskure, amma za ta gudanar da ingantaccen bincike.

A cigaban labari kuma, Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce, kotun soji ta gurfanar da mutane 12 bisa harin bom ɗin na Tudun Biri
Darakta Mai Kula da Ayyukan Yaxa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya ce, jami’an sojin Nijeriya 12 na fuskantar shari’a a kotun soji dangane da harin bom da aka kai a Tudun Biri a Jihar Kaduna.

Buba ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja kan ayyukan rundunar sojin ƙasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya tuna cewa, fararen hula 85 ne aka kashe a ranar 3 ga Disamba, 2023, bisa kuskure a hare-haren da jiragen yaqin sojoji suka kai a Tudun Biri da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Buba ya ce, rundunar za ta hukunta jami’an da aka samu da hannu a cikin lamarin na ranar 3 ga watan Disamba, inda ya ce, an gudanar da bincike tare da yanke shawarar cewa a gurfanar da jami’an da abin ya shafa a gaban kuliya, kuma a yi wa waɗanda lamarin ya shafa adalci.

“Sojoji sun gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin kuma sun fara ɗaukar matakin ladabtarwa akan waɗanda ake zargi su na da laifi.

“Haka zalika, jami’an da abin ya shafa za su fuskanci kotun soji, domin samun su da aikata laifin da ba su dace ba game da lamarin.”

Ya ce, “Ina ankare da cewa, bai dace na na yi magana da yawa game da lamarin ba, domin za a yanke hukunci a gaban kotun soji.”

Sai ya ƙara da cewa, “sojoji za su yi taka-tsantsan, don tabbatar da cewa, a nan gaba sojoji sun kiyaye kai hari kan fararen hula.”