Makamashi: Mafarki da tabbacin ’yan Nijeriya

Tare da Bashir Mudi Yakasai

Ɗaiɗaikun mutane da ɗaiɗaikun ƙasashe na da mafarke – mafarke na samun abin duniya da suka kira da abubuwa na zahiri da za a iya gani kuma a taɓa kamar makarantu, asibitoci, hanyoyi, gadoji, gidaje wato mahalli har ta kai masana’antu domin samar da ayyukan yi ga miliyoyin ‘yan ƙasa. Ƙasar Kano ita ce ƙasar farko a tarihin mulkin jama’a a dukkan ƙasar Hausa a shekara ta 1770 Miladiyya lokacin mulkin Sarkin Kano Babba Zaki Dan Yaji (1768 – 1776).

Muhammadu Babba Zaki ɗan Yaji shine mutum na farko daya gina gidaje masu ɗakuna uku-uku da soron ƙofar gida da kuma makewayi guda talatin (30) da aka bawa maƙeran Kano. Shi kuma shugaban su sarkin maƙera, Malam Yusufu maƙeri, mutumin ‘yandoya aka gina masa gida mai ɗakunan iyali shida da sararin tsakar gida da soron ƙofar gida da makewaye gida biyu. Wannan bajinta ita ce ta yaɗu a sassan ƙasar Hausa tun kafin zuwan turawa.

Yayinda Malam Yusuf Maitama ya tare a sabon gidansa na gabas da masallacin Juma’a , sai ya tara dukkan manyan dattawan maƙera, ya naɗa su sarautan qƙira kamar wazirin ƙira, galadima ƙira, madakin ƙira, wamban ƙira, ciroman ƙira da dai sauran sarautu da dama. Kowane hakimin ƙira, sarkin maqera ya ba shi gida daga cikin gidajen nan 30 da sarki ya gina.

A gidan kowane hakimi akwai maƙera da samarin maƙera, a ƙofar sarkin maƙera akwai wani ƙaton ɗaki mai ginshiƙai da yawa a cikinsa, maƙera da samarin kira sama da ɗari suke sana’ar kira har da bindigogi iri uku – madafa da aqwara da kuma tsawila. Akwai waɗanda suna amfani da harsashi, wasu kuma da alburushi. Har yau ɗin nan sunan wannan unguwa Rimin Ƙira daga qaton Rimin da ke ƙofar sarkin ƙira.

Tun daga wancan lokaci aka shiga samar da unguwoyi na sana’o’i (occupational wards) unguwar gini (builders ward) Magashi (roasting place), Takalmawa (shoe makers) Kan-karofi (Hill of dye-pits), soron dinky (hall of embroidery), Adakawa (box makers), Yan tandu (hide vessel makers), Dukawa (leather workers), Magoga (scrubers place), Majema (skin tanning place), Marina (cloth dyers) da kuma masukwani (galloping place) da dai sauransu.

Wannan shimfiɗa ce da muke yi wa matasa mu nuna musu cewa tun kafin zuwan turawa ‘yan mulkin mallaka muna da tsari na samar da masana’antu ta tattara masu sana’ar guri guda, farko samar da mahalli ga masu sana’ar da kuma gurin sana’ar. A wannan guri za a samar da zaman tare da kuma musayar fasaha da kuma kasuwa. Wannan tsari da ƙasar Kano tazo dashi ya sanya Kano tayi zarra ga dukkan sauran ƙasashen Hausa, kamar Daura, Katsina, Zazzau, Gobir, Rano, da kuma Biram har ma da banza bakwai kamar Kebbi, Yawuri, Zamfara, Gwari, Jukun, Nupe, da kuma Ilorin.

Da zamani yayi zamani da kimiyya da fasaha ta bunƙasa gano ƙarafa ya kankama kamar azurfa, da tagulla, da tama, da kuza da zinariya da kuma tsakiya da mirjani da Lu’u – Lu’u wato “Diamond”, wannan ya sanya turawan Portugal da na faransa da na Birtaniya da na Italiya da na Jamus suka lallaɓo da sunan kasuwanci wanda daga ƙarshe turawan Birtaniya suka sanya makamai suka karkashe sarakuna da hakiman su suka naɗa su, wanda ya rikide zuwa mulkin mallaka wanda har yau muna cikin sa tsundum.

Babu wani abin alheri daga zuwan Turawa Afrika da ma gida Nijeriya, su suka hana ci gaban noma da suka samemu dashi. Mu muka noma musu Auduga da gyaɗa da Rixi da kwakwar manja. Mu muka yi musu saran jeji har suka kwashi katako da suke buƙatar a masana’antun sun a ƙere–ƙeren jiragen ruwa da hanyoyin jiragen ƙasa domin su sami saukin kwasar ma’adinan da muka ambata a sama.

Zuwan turawa babu wata riba sai asara ta rufe masana’antunmu da buɗe nasu da sunan UAC, RNC, GBO, PZ, John HOIT, bata da kuma kamfanin barasa da karuwanci, baza mu manta da gidajen karuwai irinsu layin jahannama, gidan fam bakwai, layin farno-farno da kuma tudun lamarudu, dukkansu a unguwar Fagge ta Kano tun daga 1925 – 1970.

Zuwan Turawan urawan yamma annoba ce da tafi cutar kansa da cutar HIV/AIDS da kuma cutar Covic 19 a wannan zamani domin zuwansu babu abin da ya haifar sai koyar da zaman rashin amana da gaskiya illah tara dukiya ko ta wane hali. Burunsu a tara abin duniya a kira ka da kafi kowa tara dukiya wato tun daga Miloniya ko Biloniya ko kuma Tironiya da dai sauransu. Sannan kuma sun koyar da talauci da fatara da yunwa da kashe–kashe a tsakanin talakawa, to mene ne riba? Wannan shine asara bayyananniya ga Nijeriya da ‘yan Nijeriya. To lokaci yayi da zamuyi bara’a gare su.

Kada mu manta da kutun–kutun da sukayi a yayin da aka bawa ƙasar kasha, wato Soviet Union gina katafariyar masana’antar karafa “Multibilion Dollar Ajaokuta Steel Mill” duk da cewa aikin daga 1979 zuwa 1994 ya kai kashi 98% a gama, amma saboda munafurcin su aikin ya tsaya cak, komai ya taɓarɓare da yanzu Nijeriya ta na taka rawar daga cikin ƙasashe 7 da sukafi ɗaukaka a fagen masana’anta a duniya. Su suka hana tsarin shirin bunƙasa aikin noma mai suna “Green Revolution”, na shugaba Alhaji Shehu Shagari, su suka hana shirin noman Alkama na janar Ibrahim Badamasi Babangida ya tabbata.

Haka su suka hana shirin noman Rogo na Olusegun Obasanjo zama gaskiya tare da shirin noman shinkafa na Muhammad Buhari wanda suka biyo shi da yunwa da hauhawar farashin kayan masarufi.

Ƙalubalen da Shugaba Tinubu da Kashim Shettima suke fuskanta dangane da cire tallafin man fetur da sukayi da kuma qin bude kofofin shige da fice na tsandauri, inda aka kunno hauhawar farashi na kayan masarufi da abinci da tashin Dala da faduwar darajar naira da sace – sace mutane domin karɓar fansa duk daga wajen su ake shiryawa.

Domin kuwa duk wani masanin tattalin arziki tun daga ƙare yakin duniya a shekara ta 1946 zuwa yau, bai san inda akwai kaya a kasuwa kuma akwai masu saya, amma farashi yake hauhawa da abin da aka sani idan babu kaya a kasuwa kuma ga masu saya sai farashi sai ya tashi, amma yanzu akwai kaya kuma babu kuɗi a hannun masu saye amma farashi kullum ya na tashi?

Wannan shi ne abin al’ajabi a Nijeriya, an rasa wanda zai kawo maganin, “wuta daga kogi” dame za’a kashe wannan wutar? Duk wata dabara ta kashe gobara tafi ƙarfin ‘yan kwana – kwana, kamar wutar daji ce ta birnin Califonia a ƙasar Amurka inda wuta take cin ɗanyan itace kamar karmami.

Haka farashi yake tashi duk da cewa babu kuɗi a hannun masu sayen kayayyakin dake kasuwa. Wannan matsala daga jinta, matsala ce da aka ƙirƙire ta domin a haifar da tashin hankali ga gwamnati mai ci. Saboda haka wannan fili na makamashi yake kira da babbar murya ka da gwamnati ta ɗaga ƙafa wajen dawo da tallafi na man fetur duk da tsarin da zasu zo da shi, domin talakawa sun fahimci cewa wannan mafarki ne wanda ba zai tabbata ba ga waɗannan mutane. Saboda ƙarya fure take bata ‘ya’ya.