Hada-hadar kasuwar ’yan wasan ƙwallo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 29, ya ce makormarsa a Old Trafford ta dogara ne akan ko ƙungiyar ta na son ya cigaba da buga mata wasa har bayan bazara.

Newcastle United ba za bada kai ba wajan sayar da dan wasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes mai shekara 26 kan kuɗi ƙasa da fam miliyan 100 ko rabuwa da ɗan wasa mai kai hari na Sweden Alexander Isak, ɗan shekara 24.

Newcastle na son ɗaukar mai tsaron bayan Fulham da Ingila Tosin Adarabioyo mai shekara 26.

Adarabioyo, wanda AC Milan da Manchester United da Liverpool, suke zawarcinsa ya faɗawa Fulham cewa ba za isa hannu a wani sabon kwantaragi ba idan wanda yake aiki a ƙarƙashinsa ya zo ƙarshe a bazara.

Borussia Dortmund na tunanin dawo da tsohon kocinta Jurgen Klopp a 2025 bayan kocin Liverpool ya bar Anfield a ƙarshen kakar wasa ta bana.

West Ham na fatan ɗan wasan tsakiya na kasar Ghana Mohammed Kudus ɗan shekara 23 da ɗan wasan tsakiya na Brazil Lucas Paquet mai shekara 26 tare da ɗan wasan tsakiya na Mexico Edson Alvarez mai shekara 26, za su nemi zuwa wasu ƙungiyoyi a bazara.

Fluminense ta gabatar da ƙudurin sayan mai tsaron bayan Brazil Thiago Silva bayan da ɗan wasan mai shekara 39 ya sanar cewa zai bar Chelsea a ƙarshen kakar wasa ta bana.

Mataimakin kocin Feyenoord Sipke Hulshoff da shugaban kula da yadda ‘yan wasa ke taka leda Ruben Peeters da Etienne Reijnen duk sun amince su bi kocinsu Arne Slot zuwa Liverpool.

Everton na zawarcin daan wasan tsakya na Hull City da Ingila Jacob Greaves ɗan shekara 23, da kuma dan wasan gaban Blackburn Rovers da yankin Ireland Sammie Szmodics, mai shekara 28.

Juventus da AC Milan sun dakatar da zawarcin da suke yi wa Joshua Zirkzee saboda fargabar cewa ɗan wasan gaba na Bologna da Netherlands mai shekara 22 ya fi son ya koma taka leda a Arsenal a wannan bazara.

Ɗan wasan bayan Barcelona da Uruguay Ronald Araujo, mai shekara 25, na shawara akan ko ya Sanya hannu akan wani sabon kwantaragi da ƙungiyar ta Safaniya yayin da Manchester United da Bayern Munich ke zawarcinsa.

Wataƙila a tilastawa Everton sayar da mai tsaron ragar Ingila Jordan Pickford, mai shekara, 30, idan tattaunawar da suke yi da waɗanda suke yi da kamfanin 777 da ke son ya mallaki ƙungiyar ta ruguje.

Arsenal da Bayern Munich da Newcastle na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiya na Everton da Belgium Amadou Onana, ɗan shekara 22.

Manchester United na shirin ci gaba da kasancewa da kocinta, Erik ten Hag a kakar wasan da ke tafe saboda ba ta da wani zaɓi kuma idan ta kori ɗan ƙasar Netherlands to sai ta kashe maƙudan kuɗaɗe.

Arsenal ta shirya tsaf wajen sauraron tayin da za a yi wa ɗan wasan gaban ƙungiyar da kuma Brazil Gabriel Jesus mai shekara 27 a bazara.

Haka kuma Gunners na fatan ɗan wasan tsakiyar Italiya Jorginho, mai shekara 32, zai yi watsi da zawarcin da Juventus da Lazio da kuma Napoli su ke yi masa domin ya tsawaita kwantaraginsa da su.

Brighton na son ta ɗauko Kieran McKenna daga Ipswich Town idan kocinta Roberto de Zerbi ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasanni.

Tottenham na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Conor Gallagher, ɗan shekara 24, tare da ɗan wasa mai kai hari na Feyenoord da Mexico Santiago Gimenez mai shekara 23 a wannan bazarar, yayin da kuma suke son ɗan wasan bayan Bournemouth da Ingila Lloyd Kelly mai shekara 25.