Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Yayin da ya rage saura wasanni biyar a ƙarƙare La Ligar Sifaniya ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a teburin gasar da maki 73 bayan da ta tsallake Girona, wacce ke matsayi na uku da 71.
Wannan gagarumar nasara da Barcan ta samu na zuwa ne bayan da ta caskala Valencia da ci 4 da 2 a daren ranar Litinin.
Kafin tafiya hutun rabin lokaci ƙungiyar Valencia ce ke kan gaba da ƙwallaye 2 da 1.
Sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ɗan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ya zura ƙwallo uku rigis a ragar Valencia.
Ƙwallayen na Lewandowski su ne suka taimaka wa ƙungiyarsa ta yi nasara akan Valencia da ci 4 da 2.
Yanzu haka dai Barca da Girona za su kara a wasan hamayya na Catalonia a ranar Asabar.
Ƙungiyar Valencia dai da ke matsayi na takwas da maki 47, maki 2 ne tsakaninta da Real Betis da kuma maki 4 tsakaninta da Real Sociedad da suke zama na 6 da na 7, kuma suke fafatawar neman gurbin shiga gasar kofin Turai.
