Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata kotun majistare ta tsare wani limamin coci a gidan yari kan laifin yi wa wata matashiya mai shekaru 22 fyaɗe.
Babbar Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas ta tisa ƙeyar Fasto Sunday Adewoye zuwa gidan yarin ne a ranar Talaa bayan an gurfanar da shi.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙarar, Insfekta Ayodele Adeosun, ya shaida wa alqali cewa a ranar 17 ga Afrilu, 2024 ne Fasto Adewoye ya zakke wa matar da ƙarfin tsiya a garin na Badagry.
Hakan a cewarsa laifi ne a ƙarƙashin dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Legas.
Mai shari’a Patrick Adekomaiya ya ba da umarnin tsarewar ne bayan da ya ƙi sauraron roƙon Fasto Adewoye, mai shekaru 45.
Daga nan kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin samun shawara daga hukumar shari’a ta jihar.
