Anka ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta BUK

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Fitaccen marubucin littattafan Hausa da finafinan Kannywood, Malam Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi sani da ANKA ya zama shugaban ƙungiyar Hausa ta Jami’ar Bayero da ke Kano, a wani zaɓe da ƙungiyar ta gudanar ranar Jumma’ar da ta gabata 22 ga watan Maris, 2024 a zangon karatu na 2022/2023.

Marubucin wanda yake ɗalibta a Sashin Nazarin Harsunan Najeriya, inda yake karatun digirinsa na farko a fannin Harshen Hausa, ya zama shugaban ƙungiyar ne bayan zaven da aka yi masa tare da wasu masu dafa masa su goma sha ɗaya. Da suka haɗa da shi, Kabiru Yusuf Fagge a matsayin shugaba, sai Nasiru Abubakar da aka zaɓa a matsayin Mataimakin Shugaba, da kuma Hisnuddin Auwal Tahir da ya zama Magatakarda. 

Sauran sun haɗa da Umar Nasir da aka zava a matsayin Mataimakin Magatakarda, sai Isa Garba Usman Jami’in Shirye-shirye, da Khadija Yahaya Danjuma da ta zama Jami’ar Walwala.

Akwai kuma Zulaihat Safiyanu da aka zaɓa a Ma’aji, da Zubairu Ɗahiru Turaki da ya zama sabon Jami’in Hulɗa Da Jama’a na farko (PRO 1) sai aka zavi Mujahid Mansur a matsayin Mataimakin Jami’in Hulɗa Da Jama’a wato PRO II. Sabuwar Jami’ar Wayar Da Kai Da Wasanni ta ƙungiyar ita ce Amina Sunusi Shamaki, sannan Hajara Shu’aibu Muhammad ta zama Jami’ar Kuɗi. 

Ana gudanar da wannan zaɓe ne duk shekara, a kowanne zangon karatu domin samar da sabbin shugabanni, musamman saboda ‘yan aji 4 za su tafi sai a maye gurbinsu. Ana yin zaven ne ta hanyar kafa Hukumar Zaɓe, tare da bai wa ɗalibai damar yin zaɓe a junansu, ƙarƙashin kulawar hukumar makarantar.

Ana zaɓo sabbin shugabannin ne daga ‘yan aji na 1 zuwa na 4, sai dai an fi zaɓar ‘yan aji na 4 a matsayin shugaba da mataimaki ko sakatare, ya danganta.

Sabon shugaban ƙungiyar, Kabiru Yusuf Fagge ya ce ya karɓi wannan shugabanci ne domin kawo sauye-sauye da yake ganin za su canza yadda ake tafiyar da ƙungiyar a baya. Daga cikin abubuwan da yake da burin ganin ya samar domin farfaɗo da ƙungiyar Hausa ta BUK akwai shirya tarukan wayar da kai ga sabbin ɗalibai, shirya tarukan sanin makamar karatu a zangon karatu da uwa-uba shirya taron Ranar Hausa da ake yi a ƙungiyar. 

A ɗaya ɓangaren kuma yana so ya ga an gyara ofishin ƙungiyar da samar da littattafai don ɗalibai, da samar da motar zirga-zirga ta ƙungiya. Sannan idan suka kammala wannan zango na shugabancin za su shirya zaɓe, don a fitar da wasu shugabannin. 

An kafa Ƙungiyar Hausa ta BUK ne kamar sauran ƙungiyoyin jami’o’i domin haɓaka wannan sashe na Hausa aiwatar da tarukan da suka shafi cigaban harshen Hausa da al’adun Hausawa. Kuma ƙungiyar ta ɗalibai ce da za su riƙa sanin darajar ilimin da suke koyo da kuma fito da kyawawan ayyukan sashin Hausa.

Daga cikin shugabannin da suka jagoranci kafuwar ƙungiyar da inganta ayyukanta a matsayin shugabanni ko mambobi akwai wasu manyan malamai da yanzu haka ke koyarwa a wannan sashi. 

Sabon shugaban, wanda kuma ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Kwalejin Marubutan Hausa ta yanar gizo ya yi fatan shugabannin siyasa da masu hannu da shuni za su shiga su cicciɓi wannan qungiya domin ƙara havaka harshen Hausa da kawo masa cigaba.

Muna taya sabon shugaban da sauran abokan tafiyarsa murna da wannan muhimmin matsayi da suka samu, da fatan ubangiji Ya taya su riƙo, don ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.