Super Eagles ta taki sabon matsayi a jadawalin FIFA

Daga MAHDI M. MUH’D

A yanzu haka tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta taki matsayi na 33 inda ta sha gaban abokiyar hamayyarta ta yammacin Afirka a sabon jadawalin FIFA bayan da ta doke ta da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka yi a watan jiya.

Duk da cewa sau biyu tawagar Super Eagles ta Nijeriya tana faɗuwa ƙasa a sabuwar kimar hukumar ta FIFA, amma har yanzu zakarun Afirkan na gaban Ghana da ke yammacin Afirka.

Super Eagles dai ta kasance ta 28 a duniya a jadawalin watan Fabrairu amma ta koma mataki na 30 a kimar da aka fitar a ranar 4 ga Afrilu, 2024, biyo bayan cin nasarar da ƙungiyar ta samu a wasannin da ta buga a watan jiya.

Nijeriya ta lallasa Ghana da ci 2-1 a wasan farko na Finidi George a matsayin kocin riqon ƙwarya kafin ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Eagles ta Mali kwanaki kaɗan.

Sakamakon wasan da suka yi karo da juna, Super Eagles ta koma matsayi na 30 a duniya.

Duk da haka, gasar zakarun da suka lashe gasar Afirka sau uku har yanzu suna gaban Ghana, wacce ta koma matsayi na 68 a duniya.

Su ma Super Eagles na gaban Erling Haaland na Norway (47), Mohamed Salah na Masar (37) da kuma wanda zai karɓi baquncin gasar kofin duniya na gaba Kanada (49).

Har ila yau, duk da faɗuwa biyu, Nijeriya ta cigaba da zama ta uku a nahiyar Afirka bayan Morocco (13) da Senegal (17).

Masar (37), Cote d’Ivoire (38) da Tunisia (41) sun haɗa da sauran ƙasashe biyar na farko a nahiyar Afirka.

A halin da ake ciki, zakarun duniya Argentina ta ci gaba da zama ta ɗaya a matsayin jadawalin, sai Faransa da Belgium da Ingila da Brazil.

Portugal da Netherlands da Sifaniya da Italiya da kuma Croatia ne suka haɗa sauran ƙasashe goma a duniya. Za a fitar da sabunta martabar FIFA na gaba bayan hutun ƙasa da ƙasa na watan Yuni.