Kotu ta ba da belin Sirika da ‘yarsa kan N100m

Daga BASHIR ISAH

Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta ba da belin tsohon Minista a Gwamnatin Buhari, Hadi Sirika ‘yarsa tare da wasu mutum biyu kan kuɗi Naira miliyan 100 da shaidu guda biyu.

Idan za a iya tunawa hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta maka waɗanda lamarin ya shafa a kotu ne bisa zargin laifuka shida.

EFCC na zargin Sirika da yin amfani da damar ofishins wajen aikata ba daidai ba tsakanin Afrilun 2022 da Maris, 2023 a Abuja.

Kazalika, hukumar tana zargin tsohon ministan da yin sama da faɗi da biliyan N1.3 wajen ba da kwangilar Nigeria Air ga kamfanin Tianero Nigeria Limited.