Namiji ko yau ya fara mu’amalantar mace a shimfiɗa to farfesa ne a fannin – Likitar Ma’aurata

Ba laifi ko rashin so ke sa maza ƙarin aure ba – Sa’adatu Kankia

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, mun fara tattaunawa kan sha’anin ƙarin aure, inda shafin Gimbiya ya gayyato maku ƙwararru kan zamantakewar aure, wato Sa’adatu Saminu Kankia da kuma Zuwaira Dauda Kolo, wadda ku ka fi sani da Likitar Ma’aurata.
A wannan satin, kamar yadda muka yi maku alƙawari, za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. A sha karatu lafiya;

MANHAJA: Har yau dai muna kanki Sis Kolo, zancen sha’awa da ki ka yi a matsayin dalilin da ke sa maza ƙarin aure. Sau da yawa mata kan yi ƙorafin mazajensu ba su cika ɗauke masu tasu sha’awa ba yadda su suke buƙata. Kina ganin a irin hakan idan namiji ya yi aure ba zai cutar da ta ciki ba, har ma da wadda zata shigo ba, koda kuwa yana da tarin arziki?

LIKITAR MA’AURATA: Maganar namiji bai ɗauke sha’awar mace ba duk babu ita ko kuma ince bata cika tasiri ba, domin yawancin ma’aurata musamman mata ba su san bambancin jin daɗi wato (sha’awa) da kuma gamsuwa ba shi ya sa ake samun yawan matsaloli a zamantakewa, ki ji mace na iƙirarin mijinta ba ya gamsar da ita tunda ba ta san menene asalin gamsuwar ba. A haka za ki ga mace ta ginu a kai har ta kai ta ga cewa ita fa auren nan zaman dole take yi tunda ba a gamsar da ita har ta kai ta ga fara janye wa maigidan gabaɗaya shi kuma sai kiga ya ƙagu ya ƙara aure.

To a irin hakan za ki sha mamaki idan ya ƙara auren sai ki ji shi da amarya muqus saboda ya samu wadda tasan kansa ta iya, kuma take bambance tsakanin sha’awa wato jin daɗi da gamsuwar.

Shi namiji komin ƙanƙantar sa, komai rashin wayewar sa ko da kuwa bai tava sanin wacce ce mace ba aka ɗauka aka ba shi, duk ranar da zai fara mu’amala da ita zaki sameshi ‘professor’ ne a wannan fannin.

So kinga kenan ba lallai dan ta gida ta ce ba ta gamsuwa ake yarda da lallai hakan ba ne domin duk namijin da ki ka ga yana yawan maganar zai ƙara mata ko ya ƙara ɗin to gaskiya bai gaza ba.

Hajiya Sa’adatu me za ki ce ga matan da mazajensu sun yi irin yadda ki ka ce na ba su damar bayyana kishinsu tare da rarrashi, amma hakan bai sa suka sunkuya ko suka haƙura ba, asalima wasu kan qara harzuƙa ne idan ana rarashinsu, a cewarsu a bige ka ne kuma a hana ka kuka.

HAJIYA SA’ADATU: Shi ne na ce idan mace ba mai son zuciya ba ce, akwai matan da kishinsu son zuciya ne, saboda su kansu sun san mijinsu na son ƙara auren kuma ta kowacce siga yana da halin ƙarin kuma ya cancanta ya yi, kuma su kansu sun tashi sun ga kishiya a gidansu, amma a gidan miji sai su ce ba su yarda ayi ba. Irin waɗannan komai za a yi masu ba za su daina ba, sai dai kawai a bi su da addu’a, da kuma nasiha.

Sis Kolo, a ganin ki idan namiji ya aikata hanyoyin nan da ki ka ambata za a iya samun gushewar fitintinu daga uwargidan?

LIKITAR MA’AURATA: Tabbas idan ya aikata waɗannan hanyoyi za a samu gushewar fitintinu daga uwargida, sai dai idan dama sheɗaniya ce wacce bata son a zauna lafiya.

Akwai wasu sababbin ɗabi’un da mata ke bijirowa da su a yayin da aka ce miji ya ɗauri aniyyar qara aure, waxanda ke iya kai wa ga yunqurin hallaka miji ko amaryar da za a aura ko aka aura. Sis Kolo, a fahimtar ki ina wannan ɗabi’a ta samo asali ko in ce me ke kai mata ga wannan ɗanyen aikin?

LIKITAR MA’AURATA: E ba wani abu ke jawo hakan ba illa zallar sharrin shaiɗan, son zuciya da rashin sanin addini. Wasu matan kuma suna ganin sun daɗe da miji tun ba shi da ko sisi, wasu ma su suka gina mijin da dukiyarsu kuma a ce yanzu zai ƙaro abokiyar zama?

Wasu suna ganin abin kunya ne yanda suka amsa sunan su na mata kuma ace an musu abokiyar zama, aji da ƙimarsu zai ragu a idon aminan su da makusanta.

Akwai masu ganin cewa suna da kishin da idan mijinsu yazo da maganar aure da su yarda su zauna da kishiya gwara ayi haihuwar guzuma. Imma macen ta kashe mijin, ko ta kashe ita wacce za a aura, ko ta kashe kanta. Allah ya kiyashe mu.

Ki lura yawancin mazan da ba su da kirki basa riqe matansu su ba su haƙƙinsu za ki ga idan suka tashi ƙara aure matan su ba su cika jin ɗar ba saboda sun san idan ma suka shigo ai ba komai zasu rage su da shi ba tunda dama zaman ragaita suke yi.

Zama da kishiya dai dole ne ba wai don ana so ba. Waɗanne irin hanyoyi ne za ki iya shawartar mata kan tabbatar da yin su yayin da suka samu kansu a rayuwa da kishiya?

HAJIYA SA’ADATU: Akwai hanyoyi da yawa da ya kamata a ce mace ta bi yayinda mijinta ya nuna ra’ayinshi na ƙara aure. Na farko shi ne ta yi imani da Allah ta yarda da kaddara, ta sani ƙarin aure ba laifi ba ne, dama ce da Allah (SAW) Ya ba maza. Don haka yana da damar da za ya yi aurenshi.

Na biyu, ta cire tunanin baya sonta ne, ko kuma saboda ta gaza a wasu abubuwan ya sanya take son ƙara auren. Sannan ta sani ba laifi ba ne.

Sai ta kwantar da hankalinta kuma ta fahimci mijinta, ta ci gaba da yi masu addu’a Allah Ya zaunar da su lafiya ya ba shi ikon riƙe su akan adalci. Sannan mataki na gaba shi ne ta guji sauraren maganar mutane, ƙawaye da yan bani na iya, saboda lokuta da dama su ne ke hana zaman lafiya.
Sannan ta kyautata zato akan wadda za a kawo, kada ta bari shaiɗan ya yi tasiri a zuciyarta, ta riƙe girman ta da mutuncin ta ta yarda ita babba ce kuma duk wadda ya ce tana son mijinta ita ma tana sonshi. Idon ta ɗauki wannan matakin tabbas za a zauna lafiya.

Akwai zancen kashe maza da mata ke yi ba wai kan ƙarin aure ba, kan wasu dalilai da ba za a iya kiran sun isa kisan ba. A ganin ki me zai iya kai mace ga kashe abokin rayuwarta?

LIKITAR MA’AURATA: E to akwai dalilai da dama da kuma tsautsayi.
(1) Auren dole duk da yanzun ba a cika yi ba, shima yana taka rawar gani wajen ingiza mace ta kai ga kashe miji domin dama bata son mijin aka ɗauka aka bata a haka ta dinga zama tana shanye duk wani abu ba tare da ta gudu ba domin tsoron iyayenta. So abu kaɗan ya yi yunƙurin yi sai kiga ta ɗauka babba wanda har za ta kai zuciyar ta ga aikata kisan

(2)Kishi mummuna: wanda Allah ya hana, sai ki ga mace ta ƙudura ita kaɗaice da miji domin haka ko waya miji bai isa ya yi da wata ba bare azo batun ƙarin aure sai ki ga mace ta kashe miji.

(3) Izayar miji: wani mijin za ki ga yana da mugun hali na ƙuntatawa macen gida musamman idan ya ƙyallara ido ya hango wata wacce yake ganin tafi matar. Azabar yau dabam, na gobe dabam, wani ma mashayi ne idan ya shigo a bige haka zai kusanceta babu wani rarrashi, idan kuma ta kuskura ta yi yunƙurin bijirewa to sai duka da wulaƙanci, to wasu matan garin ƙwatar kansu ya haɗu da mummunar ƙaddara sai kiga ta kaita ga kashe miji.

(4) Auren sha’awa: mijin da zai auri mace kawai domin sha’awa saboda haka a daren farko idan ya gama sauke wannan sha ‘awar to shikenan ta zama da ita da mutum mutumi ɗaya, sai dai ya koma bin wasu a waje.

Wani ma har gidan zai dinga kawo mata ko ya kira su a gaban matan babu yadda ta iya. To idan aka samu wacce bata miƙa lamura ga Allah sai kiga zuciya ta ɗebe ta ga kashe mijin. Akwai dalilai masu yawa waɗanda lokaci bazai bamu dama mu fayyace su anan ba.

Wasu na ganin duk mace ta kashe mijinta da suka jima a tare to tura ce ta kai bango, ma’ana ba dalilin da ta faɗa ba ne kawai ya kaita ga aikata hakan ba, cin zarafi ne da ya jima yana yi mata ne ya taru ya kaita ga hakan. Menene ra’ayinki kan wannan fahimtar?

LIKITAR MA’AURATA: E ƙwarai idan tura ta kai bango ne, amma gaskiya yawancin mata yanzu masu kashe mazajen za ki samu zallar son zuciya ce.

Wasu kuma su kansu matan ‘yan shaye shaye ne kawai. Wasu matan kuma dama sun auri mijin ne da wani manufa ko na dukiyarsa, to idan suka shiga suka tarar ba haka ba ma’ana dukiyar mijin ba na ci ba ne sai kisa

Wasu matan kuma ƙyashi ne su kar miji ya kula mahaifiyarsa ko ya kyautata mata musamman idan ya dawo sai ya fara bi gidan mahaifiyarsa, idan ma zai fita sai yabi ya duba ta, sannan ‘yan uwansa zasu zo ya yi musu hidima, ita wannan ne bata so daga nan aure bai wani daɗe ba sai kiji mace ta kashe miji.

Wata macen kuma dama ‘yar daba ya aura bai sani ba wanda ko a gidansu ba a kwaɓarta bare a mata faɗa, yasa da zaran ta haɗu da mijin da zai tashe ta da safe ya ce ta yi kaza da kaza, ko tashi kiyi wallahi ba kya salla akan lokaci, a a ga wanki na wanke min, dafa min abinci da sauransu sai kiga ta kai ga kisa saboda tana ganin ai mijin ya takura ta.

Wata kuma wani mijin ne a cikin ranta ba mijin da ta aura ba, idan miji ya fita wancan ɗin yana kiran ta ya hure mata kunne da kalamai na ingiza mai kantu ruwa.