Ni ban ɗauki rubutun batsa a matsayin matsala ba – Mukhtar Yakubu

“Rubutu abu ɗaya ne, abin da za a rubuta ne ke bambanta su”

Daga AISHA ASAS

A wannan karon dai shafin adabi ɗan gida ya ɗauko maku, domin mun tattauna ne da ɗaya daga cikin daɗaɗɗun wakilan Manhaja, kuma marubuci da ya rubuta littafan hikaya da kuma na addinin Musulunci.

A tattaunawar mai karatu zai ji yadda ɗan jaridar ya rikiɗe zuwa marubucin ƙagaggun labarai da kuma dangantakar da ke tsakanin aikin jarida da rubutun labari.
Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mukhtar Yakubu;

MANHAJA: Duk da kai ba baƙo ba ne a Manhaja za mu so jin tarihin ka.

MUKHTAR YAKUBU: To a wannan fage zan iya kiran kaina a matsayin baƙo ko a kira ni da baƙon, saboda a yanzu za a yi mini tambaya ne a wani ɓangare na rayuwata, wato harkar rubutun littafi. To kamar yadda aka fi sani na a harkar rubutun littafi sunana Mukhtar Yakubu, Kano wanda a aikin jarida nake takaitawa da Mukhtar Yakubu, kuma ni ɗan Jihar Kano ne a nan aka haife ni a shekarar 1976 Kuma Kano na tashi da girma duk wasu harkoki nawa na yarinta da harkar karatu na addini da na boko duk a Kano na yi su kuma har yanzu ina zaune ne a cikin garin Kano ni da iyalina.

Yaushe ka fara rubutu?

To ita harkar rubutu zan iya cewa ɓangare biyu ce. Akwai rubutu na littafi akwai kuma rubuta labarai da rahotanni da nake yi a jaridu da mujallu kuma dukka biyun an sanni da su tsawon lokaci. Kuma ko dai su zama suna tafiya ne a tare ko wani ya samar da wani.

Kamar dai rubuta littafi karatu da kuma rubutu a jaridu shi ne ya samar da shi wanda na kasance mai karanta jaridu da mujallu a shekarun 1990 lokacin Ina yaro kenan nake karanta jaridu irin su Gaskiya ta fi Kwabo, Almizan, Nasiha, Ayau, Rana, da sauransu wanda a wannan lokacin na samu damar rubuta wasiƙu ina turawa ana bugawa da haka har na zo ina yin sharshi da sauransu.

To a nan na fara yin rubutu a jarida har na saba da shi wanda hakan ya bani damar fara rubuta ƙagaggun labari saboda karanta muhawar da ake yi a kan adabin kasuwar Kano tsakanin su Ibrahim Malumfahi, da Ibrahim Sheme, Danjuma Katsina, Kabiru Assada, Ado Ahmad Gidan Dabino, da sauransu. Wannan ya haifar da rubuta littafina mai suna ‘Mijina ne’ na 1-2 . Wanda aka buga shi ya fito kasuwa a 2005.

Amma dai daga wannan sai ba koma rubutun addini da kuma tarihi wanda rubuta littafina ‘Hijira zuwa Habasha’ ‘Ashabul fili’ ‘Nafilolin Azumi da addu’o’i’ ‘Tarihin Sayyadina Aliyu’ ‘Tarihin Sayyada Zainab’, dai sauransu. Kuma daga baya a 2015 sai na kuma rubutun soyayya inda na rubuta ‘Haske So’ ‘Fagen So’, ‘Farin Cikin Masoya’ ‘Maigida’.

A kwanakin nan muka ga wani sabon littafinka na yawo a kafafen sada zumunta. Shin littafin ya shiga kasuwa ne ko da saura?

E to shi wannan littafin ta ɓangaren kasuwa za a iya cewa sabo ne kuma ba sabo ba. Saboda littafin yana da tsawon tarihin rubutawa don haka na mayar da shi kamar wani bakandamiya a cikin littattafaina. Saboda shi wannan littafin farko na fara buga shi ne tun a 2005 wanda a lokacin na yi shi shafi 32 aka sayar da shi sosai a kasuwa kuma don na san a lokacin an buga kwafi ya fi 5000 har zuwa lokacin da kasuwar littafi ta mutu a kasuwar Kurmi.

To sai kuma na yi tunanin samar masa da wata kasuwar , don haka na ƙara shi ya koma shafi 64 kuma na yi wasu gyare-gyare, saboda na ƙara ilimi da kuma shekaru. Wani daga cikin ilimin da na qaru da shi a lokacin shi ne rayuwar aure da zama da iyali, domin a lokacin da na fito da na farko a 2006 ban yi aure ba.

Amma a 2015 na yi aure ina da iyali don haka sai na ga wasu abubuwan da na rubuta duk da bincike na yi akwai shirme a cikin su don haka sai na gyara na kuma ƙara wasu abubuwan da na ƙara ilimi a kansu na zamantakewar iyali shi ma na fito da shi aka ci kasuwar sa a lokacin har zuwa lokacin da takarda ta yi tsada buga littafin ya zama ko kana da halin ka buga, to idan ka buga kuɗin ka ba zai dawo ba na tattara na haƙura.

Sai kuma daga baya na ƙara tunanin na ƙara faɗaɗa bincike don na samar da wani babban littafi da zai zama kundin zamantakewar ma’aurata wanda ko da ban samu damar buga shi ba zan bar wa ‘yan baya in da rabon zai fito sai a samu wani ya buga shi. Kuma cikin yarda da Allah littafin mai shafi 200 sai ga shi na kai ga buga shi har ma ya shiga kasuwa an fara sayar da shi.

Sunan littafin ya ɗauki hankalin mutane musamman ma ma’aurata. Ta ya ka samar da sunan?

To shi sunan wannan littafin zan iya cewa ya faro ne daga wani rubutu da na yi aka buga a Mujallar Nishaɗi wadda Bala Makosa yake a matsayin edita kuma mawallafi a 2003. Daga wannan rubutun da na yi na samar da sunan littafin, don ko shi rubutun da na yi a wancan lokacin ya tayar da quda saboda ana cewa na fito da wasu bayanai na ilimin jima’i wanda ya kamata a ɓoye su.

Ko sunan da abin da yake ciki na da kamanceceniya?

Gaskiya zai iya zama hakan. Domin wasu sirruka ne na zaman aure aka taskace su wanda zai amfanar da rayuwar aure tun daga lokacin neman auren da yadda ake ƙulla shi da siga da shaidu. Kuma akwai ɓangaren gyaran jiki ga kwalliyar mata da yadda ya kamata miji ya kasance da matar sa ta na amarya da sauran abubuwan da suka shafi zaman aure..

Wannan littafin naka ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sa. Ko za mu iya sanin abin da ya ƙunsa?

To kamar yadda na fada ne a baya sai dai na ƙara da cewar akwai abubuwan da aka rubuta na daga haƙƙoƙin da ke tsakanin ma’aurata ta fuskar addini da kuma na maslahar wajen da mutum yake rayuwa. Wanda idan za a yi zaman aure na gaskiya sai an duba yadda rayuwar aure take a wajen da ma’aurata suke.

Yanzu kamar yin girki ga mace, mu a wajen mu kyautatawa ce ta wajibi wadda idan mace ba ta yi girki a gidan mijinta ba sai a kai ga rabuwa, amma a wasu ƙasashe ba haka ba ne. To irin wannan da makamantan su duk an kawo su domin da mata da miji kowa ya san matsayin sa a zaman aure.

Me ya sa ka zaɓi yin littafi a kan zamantakewar aure?

To ni marubuci ne na kowanne ɓangare na yi rubutun soyayya tarihin Muslumci. Ko a lokacin da Amurka ta mamaye Iraƙi karo na biyu wanda da shi ne aka kawar da Gwamnatin Saddam Hussaini na rubuta littafi mai suna ‘Gumurzu a Iraqi’ 1-2 don haka ina yin rubutu ne a dukkan ɓangarori na rayuwa.

An san ka a matsayin ɗan jarida ko ya ya bambamcin rubuta labarin jarida yake da na littafi?

To rubutu dai abu ɗaya ne, sai dai abin da za a rubuta ne yake bambanta su. Kamar rubutun jarida wani ilmi ne mai zaman kansa haka shi ma rubutun littafin ko na soyayya ne ko na tarihi ne ko ma dai na menene.

Amma shi rubutun jarida shi na fi kusanci da shi yau da kullim musamman a kan abin da ya shafi labarin nishaɗi kamar na ‘yan fim, mawaƙa da sauransu. Don na shafe kusan shekara 20 Ina matsayin babban wakilin Mujallar Fim a Kano wanda ba na jin akwai wani mai bada labari a Mujallar Fim tun daga farkon kafa ta a1999 da ya kaini daɗewa a matsayin wakilin mujallar, duk da na riqe wasu ayyukan a kamfanin amma an fi sani na a matsayin wakilin Mujallar Fim.

Haka na Manhaja tun da aka samar da ita na fi bayar da labarin nishaɗi har zuwa yanzu. Kuma na yi zamani da Leadership Hausa ita ma tun fitowar ta ga Mujallar Muryar Arewa ta Kabiru Assada, da sauran, duk da ma dai a yanzu harkar onlayin ta cinye jaridu da mujallu.

Wanne lokaci ne ka fi sha’awar yin rubutu?

Gaskiya na fi sha’awar yin rubutu cikin dare. Don in ba wani abu ya kawo mini matsala ba. Zan iya kwana a zaune ina rubutu.

A naka hange wa za ka iya kira da marubuci?

To marubuci dai shi ne wanda zai iya rubuta abin da za a karanta a fahimci saƙon da yake so ya isar a kowanne ɓangaren yake rubutun kuwa.

Mun kawo lokacin da marubuta suka yawaita sakamakon onlayin. Shin a ganin ka ci gaba ne ko ci baya?

Wannan ci gaba ne sosai musamman ta ci gaban zamani, domin in ba ta onlayin ɗin ba wani ba zai samu damar isar da saƙon sa ba. Haka su ma masu karatun in ba ta hanyar onlayin ɗin ba, ba za su samu damar su karanta ba.

Matsalar yawaitar rubutun batsa ina matsalar ta samo asali?

To shi rubutun batsa ba za ka raba shi da zamantakewar mutane ba, sai dai idan an yi rubutun cikin rashin ilimi, amma idan an yi da ilimi akwai faɗakarwa a ciki. Kuma su masu cewar ana rubutun batsa da sunan cewa su malamai ne, ai yanzu muna ganin sun cika shafukan Tik Tok suna faxar abubuwan da mu masu rubutun ba ma rubutawa. Amma da yake sun ɗauki abin sun cusa shi a cikin addini sai aka ɗauka addini suke koyarwa, kuma da yawa mun fi su ilimin abin, amma saboda sun raba abin da addini sai ya zama ana kallon masu faɗakarwa ta addini kuma mu’amala ce ta rayuwa haka muke magana a kai.

Ya ka ke ganin za a iya kawar da matsalar rubutun batsa?

To ni ban ɗauki rubutun batsa ba a matsayin matsala ba. Inda matsalar take sai dai idan za a yi shi bisa jahilci to gaskiya a nan ba na goyon bayan hakan.

Marubuta masu tasowa, wanne kira za ka yi gare su?

To kira na shi ne su yi rubutu domin isar da saƙo wanda ko bayan ransu za a tuna da su a shi musu albarka, kuma su rayu cikin mutunci.

Ko akwai wata shawara da ka ke da ita ga marubuta bakiɗaya?

To shawara dai ita ce a nemi ilimi a kan abin da za a rubuta kuma ka sani Allah zai tambaye ka a kan abin da ka rubuta.