Adadin yaran da ba sa tafiya makaranta ya kai miliyan 18 a Nijeriya — UNICEF

Daga BASHIR ISAH

Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin (UNICEF) ya koka kan yadda ake samun ƙaruwar yaran da ba sa tafiya makaranta a Nijeriya, tare da cewa, yanzu adadin waɗannan yara ya kai miliyan 18.3.

Ya ce wannan adadi ya sa Nijeriya ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa a faɗin duniya yawan yaran da ba sa tafiya makaranta.

Babban Jami’in UNICEF a Bauchi, Dokta Tushar Rane, shi ne ya bayyana haka a wajen taron masu ruwa da tsaki na yini biyun da aka shirya a Gombe kan batun ƙananan yaran da ba sa tafiya makaranta da sauransu.

Jami’in ya ce, “Abin takaici ne ganin yadda wannan adadi ya sa Nijeriya ta zama ƙasar da ta fi kowacce fuskantar ƙalubalen yaran da ba sa tafiya makaranta a faɗin duniya.”

Ya ƙara da cewa, a halin da ake ciki, kashi 63 na yaran da suka kai shekarun shiga firamare kaɗai ke tafiya makaranta yadda ya kamata a ƙasar.

Yayin da yake ci gaba da bayyana damuwarsa, jami’in ya kuma ce kashi 84 kaɗai ke samun zarafin shiga sakandare bayan kammala matakin firamare.

Rane ya ɗora alhakin ƙaruwar wannan matsalar a kan rashin tsari mai inganci da rashin ware kaso mai tsoka wa ɓangaren ilimi, ƙarancin malamai da azuzuwa da dai sauransu.

Domin magance wannan matsalar kuwa, UNICEF ya ce yana ƙoƙarin yin haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko wajen samar da ingantaccen tsarin da zai taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa tafiya makaranta a faɗin ƙasar.