Dortmund ta fitar da PSG daga gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Borussia Dortmund ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai, bayan da ta yi nasarar cin Paris St Germain 1-0 ranar Talata a Faransa.

Ƙungiyoyin sun je hutu babu ci ko ɗaya, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta ci ƙwallo ta hannun Mats Hummels.

A ranar Talata a makon jiya a wasan farko a daf da ƙarshe a Jamus, Dortmunda ta yi nasara 1-0, kuma Niclas Fullkrug ne ya ci mata ƙwallon tun kan hutu.

Kenan Dortmund ta kai wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai ta bana da cin ƙwallo 2-0 gida da waje.

Wannan shi ne karo na huɗu da suka haɗu a bana a gasar zakarun Turai tsakanin Dortmunda da PSG, waɗanda suka fara fuskantar juna a rukuni na shida.

Cikin Disambar bara Dortmund da PSG suka tashi 1-1 a wasa na biyu, bayan da PSG ta ci 2-0 a wasan farko a cikin rukuni cikin watan Satumba.

Kawo yanzu sun fafata a tsakaninsu sau takwas, inda Dortmund ta yi nasara uku da canjaras uku, yayin da PSG ta ci karawa biyu.

Dortmund ta ɗauki Champions League ɗaya a 1996/1997, yayin da PSG har yanzu ba ta samu ɗaukar kofin ba.

Ƙungiyar Jamus za ta jira wasan ƙarshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Real Madrid da Bayern Munich ranar Laraba.

Ranar Talata ta makon jiya aka tashi 2-2 a Jamus a wasan farko na daf da ƙarshe a gasar zakarun Turai tsakanin aungiyar Jamus da ta Sifaniya.

Real Madrid, wadda ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla na fatan ɗaukar gasar Zakarun Turai na 15 jimilla bayan cin Bayern.

Ita kuwa Bayern Munich, wadda ba ta ɗauki Bundesliga a bana ba tana da kofin zakarun Turai shida a tarihi.

A qarshen kakar bana Kylian Mbappe, wadda ya lashe kofin duniya da tawagar Fransa, wanda bai tava lashe kofin zakarun Turai ba, zai koma Real Madrid.