Sabuwar manhajar KIPPIS za ta bada cikakkun bayanai akan ma’aikatan Kano – AG Abdulkadir

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Akanta Janar na Jihar Kano, Abdulqadir Abdulsalam ya bayyana cewa ƙirƙiro da manhaja KIPPIS da gwamnatin Jihar Kano ta yi zai taimaka wajen samun cikakkun bayanan ma’aikatan jihar.

Abdulsalam ya bayyana hakan ne ranar Talata lokacin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske bayan kammala taron kwana biyu kan yadda sabuwar manhajar tattara bayanai na ma’aikatan Kano da ake kira KIPPIS da aka yi a jihar Kano wanda ya ƙunshi ofishin Akanta Janar da Ofishin kula da ma’aikatan Kano da ofishin binciken kuɗi na Kano da ofishin kula da biyan albashi da gwamnan Jihar Kano ya kafa da ake kira Payroll Salary Standard Committee PSSC da dai sauran masu ruwa da tsaki.

Jihar Kano ta samar da sabuwar Manhajar KIPPIS ne don tattara bayanai akan ɗaukacin ma’aikatan gwamnatin da na ƙananan hukumomin har ma da ‘yan fansho na Jihar Kano baki ɗaya, wannan shi ne babban aikin manhajar Kano State Integrated Personal and Payrolls Information System KIPPIS a taƙaice.

Har ila yau ya ce baya ga bayanan ma’aikatan da na ƙananan hukumomin da ‘yan fansho haka kuma za a yi amfani da Manhajar KIPPIS za a yi amfani da ita wajen haɗa manhajar da hukumar kula da lafiya ta KACHMA domin kula da lafiyar ma’aikata ta hanyar zava asibitin da suke so ya kula da lafiyarsu bisa la’akari da wancan tsari na baya da wasu ma’aikatan ana ɗaukar kuɗinsu amma ba sa cin gajiyar kuɗin su amma wannan tsari na sabuwar manhajar zai bada dama kowanne ma’aikaci ya ci gajiyar kuɗinsa kamar yadda aka tsara a wannan lokaci.

A ƙarshen AG ya tabbatar da cewa haka manhajar za ta taka muhimmiyar rawa wajen harkar ilimin firamare ta yadda ma’aikata za su yi amfani da wannan KIPPIS wajen kula da ilimin ‘ya’yan su da zaɓin makarantun firamare da suke buƙata haka kuma za a yi amfani da wannan manhaja domin haɗa ta da ma’aikatar kula da lafiya ta tarrayya da makamantansu yadda dai ma’aikata za su ci gajiya ta hanyar yin rijista domin samun horo da gogewa a kan al’amura da za su samu ci gaba na ilimi na aiki da rayuwa.

Inda kuma ya yabawa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf kan irin ƙoƙari da ya ke na bunƙasa har kuɗin shiga wanda idan al’umma Kano ta bada kyakkyawan haɗin kai da ƙoƙari na ma’aikata ba shakka Kano za ta iya dogaro da kanta da ikon Allah ya kuma nemi haɗin kan al’ummar Kano da addu’o’in su domin ci gaban Kano na zaman lafiyan Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.