Cibiyar Horti ta horar da masu saida kayan amfanin gona a Kano

Daga MAHDI M. MUH’D

A ƙoƙarinta na bunƙasa noman kayan lambu, Cibiyar Horti Nijeriya wacce ƙasar Dutch ta ke tallafawa ta horas da masu sayar da kayan amfanin gona a Jihar Kano.

Taron bitar ya gudana ne a ranar Larabar da ta gabata, a inda aka zaƙulo ’yan kasuwar a qananan hukumomi daban-daban na Jihar Kano waƙanda suka haƙa da Kumbotso, Rimin Gado, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Tofa, Garko, Bichi da kuma Minjibir.

Wannan horaswa dai wani yunƙuri ne na ƙarfafa noman kayan lambu da kuma ilimantar da kananan masu sayar da kayan amfanin gona.

Taro dai ya mayar da hankali ne wajen yadda yan kasuwar za su tsara kasuwancin su ya tafi dai dai da zamani. 

Haka nan kuma Hoti Nijeriya a yanzu tana ilimantar da ‘yan kasuwar a kan yadda za su sayar da maganin cutar tsutsar tumatir mai suna TUTA ABSOLUTA tunda yan kasuwar za su taka muhimmiyar rawa wajen sanar da manoma yadda zasu yi amfani da maganin.

Ɗanjuma Makama wani ƙwararan masanin kasuwanci a Horti Nijeriya yayi ƙarin haske kan al’amarin “burin mu a wannan horaswar shi ne mu ƙarfafafi yan kasuwar a kan kasuwancin nasu yadda zasu samar da sakamako mai kyau a fagen kasuwanci kayan amfanin gona a faɗin Jihar Kano ta yadda za mu samar musu da muhimman kayaiyaki tare da ilimin da suke buƙata.”

Munir Yawale yana daga cikin waɗanda aka ba su bitar ya ce mun ƙaru sosai daga Horti Nijeriya musamman yadda suke nuna mana yadda zamu gudanar da kasuwancin mu ta yadda zamu riƙa koya wa manoma yadda za su yi amfani da magungunan da suke saya a wajen mu, musamman wannan cuta ta TUTA ABSOLOTA wacce take yiwa tumatir mummunar illa.