Falastinawa 32,200 aka kashe a Gaza – Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa, a ranar 174 na yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al’ummar Palastinu, kimanin Falastinawa 32,200 ne sojojin mamaya na Isra’ila suka kashe.

Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis. 
Sanarwar ta ce, “a da Gaza ta kasance kurkuku ga al’ummarta, a yau kuwa ta zamo maƙabarta ga al’ummarta. Maƙabarta ga dubun dubatar mutane kuma maƙabarta ta hana ‘yancin ɗan adam.”

“Babu wata hujja ta cigaba da sayar da makamai ga Isra’ila. A cikin watanni shida da suka gabata, Isra’ila ta tabbatar da cewa tana amfani da makaman ƙasashen yammaci wajen kashe al’ummar Palastinu ba. Me ya sa ƙasashen Yamma ke ci gaba da ba su makamai?”

“Falastinawa a Gaza yara, mata, maza sun kasance maƙale a cikin azaba. An shafe al’ummomi. An rushe gidaje. An shafe ahali baki ɗaya. Tare matsananciyar yunwa da ke addabar al’umma, abin ban tsoro ne cewa bayan shan wahala na tsawon watanni, Falastinawa a Gaza suna azumin watan Ramadan cikin fargabar faɗowar bama-bamai na Isra’ila, harsasai suna tashi ko ina, har yanzu ana ta luguden wuta, an hana shigowar taimakon jinƙai”, inji sanarwar.

A cewar ma’aikatar lafiya ta Falastinu, ya zuwa ranar Lahadi 24 ga watan Maris, kimanin Falastinawa 32,200 ne sojojin mamaya na Isra’ila suka kashe.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Daga cikin waɗanda abin ya shafa, kashi 72 bisa 100 mata ne (kusan 8,800) da yara (kimanin 13,750). Bugu da ƙari, kusan Falastinawa 74,500 ne suka jikkata, wanda akasari mata ne da ƙananan yara.

An kiyasta cewa sama da mutane 8,100 ne suka vace a ƙarƙashin varaguzan ginin.”

“Dakarun mamaya na Isra’ila (IOF) sun kai hari a asibitin Al-Shifa, lamarin da ya yi sanadin jikkata da asarar rayuka a tsakanin majiyyata, da ma’aikatan lafiya, da kuma ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka a wurin.

“Aƙalla fararen hula 27, da suka haɗa da yara 23 da tsofaffi, sun mutu sakamakon rashin ruwa da rashin abinci mai gina jiki a asibitin Kama Adwan da ke Arewacin Gaza. Don ƙara cin zarafi, mamayar Isra’ila ta yi amfani da hana shigar da manyan motocin agaji gabaɗaya,” inji sanarwar.

“Ya zuwa ranar Litinin, 25 ga Maris, adadin Falastinawa da aka kama a cikin watanni 6 da suka gabata sun kai 7770 a Yammacin Gavar Kogin Jordan da aka mamaye. Wannan ya haɗa da mata 250, ciki har da matan Falastinawa da aka kama daga ƙasar 1948, da kuma matan Gazawa da aka kama a cikin OWB. Bugu da ƙari, an yanke wa yara 500 da ‘yan jarida 23 hukuncin ɗaurin rai-da-rai, tare da bayar da umarnin tsare mutane sama da 4400.”

Sanarwar ta ce, “Ya zuwa ranar 20 ga Maris, Palastinawa miliyan 1.7 (sama da kashi 75 cikin 100 na al’ummar ƙasar) sun yi gudun hijira a duk faɗin Zirin Gaza. Ana tilastawa iyalai yin ƙaura don neman tsaro. Bayan ƙazamin harin bama-bamai da faɗan da Isra’ila ta yi a Khan Younis da yankin Tsakiya cikin ‘yan makonnin nan, adadin mutanen da suka rasa matsugunansu sun koma kudu.”

“Rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara yana yaɗuwa cikin sauri kuma yana kaiwa ga munanan matakan da ba a taɓa ganin irinsa ba a zirin Gaza saboda yawaitar tasirin yaƙin da ci gaba da taƙaita kai kayan agaji,” inji sanarwar.