Sama da shanu 300 aka sace mana cikin makonni uku a Jihar Filato – Makiyaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Makiyaya a Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato, sun koka cewa ɓarayin shanu sun arce musu shanu sama da 390 da kudin su ya kai aƙalla Naira miliyan 300.

Makiyayan sun ce an yi awon gaba da shanun a lokacin da suke kiwo a Bot, Faranti, Anguwan Abuja, Makada da Wumat.

Manhaja ta buga cewa shugaban ƙungiyar ci gaban Fulani na ‘Gan Allah’ dake qaramar hukumar Bokkos Saleh Adamu ya ce sun kai ƙarar abinda aka yi musu zuwa ga kwamandan sashin ‘Operation Safe Haven’ da ke yankin.

“A ranar 4 ga Maris, an yi awon gaba da shanu 71 a yankin Bot, sai a ranar 11 ga Maris, wasu ‘yan bindiga suka saci shanu 93.

“An sace shanu 73 ranar 17 ga Maris sannan aka ƙara arcewa da wasu a Anguwan Abuja ranar 22 ga Maris.

“An saci shanu 55 a ranar 31 ga Maris da wasu shanu 100 a unguwar Wumat.
A jawabinsa, shugaban qungiyar GAFDAN na Jihar Filato, Garba Abdullahi, ya ce an kai wa ‘yan ƙungiyarsu hari.

“Ana sace mana shanu yadda aka ga dama, baya ga shanu 390 da aka sace a Bokkos, mun kuma yi asarar shanu sama da 100.”

Shugaban ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta kawo ɗauki ga Fulanin jihar Filato.