Hajjin 2024: Gwamnan Jigawa ya bada tallafin Naira miliyan ɗaya ga kowane maniyyacin jihar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya sanar da bayar da tallafin Naira miliyan ɗaya ga maniyyata aikin Hajji daga jihar.

Kakakin hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Jigawa Murtala Usman ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

Usman ya ce an bayar da tallafin ne ga maniyyatan Jigawa da suka fara ajiyar kuɗaɗen aikin Hajjin su na 2024 tun a baya.

“Kowane maniyyaci yanzu zai biya cikon Naira 900,000 kawai saɓanin Naira miliyan 1.9 da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sanar.

“Tun da farko hukumar ta NAHCON ta ware kujeru 1,518 ga jihar Jigawa, amma kujeru 1,260 kacal aka sayar wa maniyyatan da suka yi niyya kuma sun kammala biyan kuɗaɗensu.

Ya ce gwamna ya tallafa wa waɗanda suka daɗe da fara ajiyar kuɗaɗen tafiyar su ne tun a baya. Maimakon naira miliyan 1.9 da za su cka, yanzu sai dai su cika naira 900,000.

Da yawa daga cikin wasu mazauna garin Dutse da wasu ƙananan hukumomin jihar sun yi wa gwamna Namadi, amabliyar addu’o’i domin nuna farin cikinsu ga wannan ƙoƙari da tallafi da ya yi wa mutanen jihar.

Gambo Lawal ya bayyana wa Manhaja cewa wannan abin farin ciki ne kuma abin a yaba wa gwamna Namadi.

”Mu dai a jihar Jigawa mun yi dacen gwamna. Duk inda kake tunani gwamna Namadi ya wuce nan. Miliyan ɗaya ba ƙaramin kuɗi ba ne a ce an cika maka ka tafi aikin Hajji. Allah ya saka masa, Amin.”