Yanzu-yanzu: NERC ta ci AEDC tarar N200m kan saɓa dokar sabon farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ta ci kamfanin raba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Plc, (AEDC), tarar Naira miliyan 200 saboda saɓa dokar sabon farashin wutar lantarki.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da NERC ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a.

A cewar NERC, an ci AEDC tara ne saboda ƙin yin aiki da ƙa’idojin sabon farashin wutar lantarki wanda hakan ya haifar da ruɗani a tsakanin kostomomi da masu ruwa da tsaki a masana’antar lantarki.

Ta ƙara da cewa, ta ɗauki wannan mataki ne biyo bayan bibiyar da ta yi da kuma ƙorafin da ta samu daga kostomomi inda ta gano AEDC ya yi amfani da sabon farashin a kan dukkan rukunin masu amfani da wutar lantarki maimakon taƙaitawa a kan rukunin da aka ayyana.

Daga nan, hukumar ta buƙaci AEDC da ya mayar wa kostomomin rukuni ko kuma Bands B, C, D da E kuɗin wutar da ya caje su ba bisa ƙa’ida ba.

A ranar Alhamis NERC ta sanar da ƙarin kuɗin wutar lantarki amma ga rukunin masu amfani da wuta na ‘Band A’.