Gwamnati ta ba wa jaruma Rahama Sadau muƙami a kwamitin IDICE

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarrayya ta ba wa jaruma Rahama Sadau muƙami a sabon kwamiti ƙarƙashin ƙungiyar zuba jari a harkar ƙirƙira da sadarwar zamani, wato IDICE.

Kwamitin wanda ya kasance a layi na biyu a muhimmanci kan abinda ya shafi ƙirƙira da fasaha.

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin ne don ƙaddamar da ƙungiyar ta bunƙasa harkokin fasaha da ƙirƙira tare da saka hannun jari.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jinjina wa wannan mataki na cigaba a Nijeriya.

Shirin IDICE haɗaka ce da gwamnati, abokanan cigaban duniya kamar African Development Bank, French Development Agency, da Islamic Development Bank.

Burin ƙungiyar dai shi ne taimako da inganta aikin ƙirƙira da amfani da yanar gizo.

A yayin zaman mitin ɗinsu a watan da ya gabata, NEC sun amince da fitar da dala miliyan 617.7 na shirin a duk garuruwa 36 da ke Nijeriya da birnin tarayya.

A lokacin ƙaddamar da kwamitin a ranar Laraban da ta gabata, mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya jaddada amfanin wannan ƙungiyar wurin gina vangaren ƙirƙira da amfani da yanar gizo.

Ya ce, “Mun ɗauki hanyar cigaba, haɗin kai da kuma samun dama. Tafiya wadda ke riƙe da girman canza fuskar ƙirƙira da fasahar na ƙasarmu.”