An kama mai sayar da yalo kan zargin yi wa yaro fyaɗe a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an ‘yan sandan jihar Bauchi da ke aiki ƙarƙashin rundunar maido da zaman lafiya sun kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya yi wa wani yaro ɗan shekara goma fyaɗe.

Matashin da ake zargi ya yaudari yaron da naira 30 da alawa inda ya nemi yaron ya raka shi wani kango da ke bayan wani gidan mai a kan titin Kofar Ran domin ya yi bahaya.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar ta ce bayan ya yi bahayar ne kuma, matashin ya bukaci yaron da ya tuve wandonsa ya duba ko ya yi tsarki.

A cewar sanarwar, bayan da yaron ya cire wandonsa ne kuma, matashin ya cakumo yaron ta baya inda kuma ya yi masa fyaɗe.

Sanarwar ta ƙara da cewa “nan ne yaron ya ruga wajen shugaban gidan man tare da sanar da shi abin da matashin ya yi masa.”

Rundunar ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa matashin da ake zargi ya fito daga ƙauyen Jingino da ke ƙaramar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Ya je jihar Bauchi shekara biyu baya inda yake sana’ar sayar da ɗata a gidan man da ke kan titin Kofar Ran, in ji sanarwar.

Rundunar ta ce an gano cewa matashin mai sayar da ɗata ya yi amfani da yanayin yaron da yake da matsalar ƙwakwalwa wajen yi masa aika-aikar ta fyaɗe.

‘yan sanda sun ce an garzaya da yaron zuwa asibitin koyarwa na Bauchi tare da matashin da ake zargi inda aka gudanar da gwaje-gwaje domin duba lafiyarsa.

Ana ci gaba da yin bincike kuma da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban kotu.