Sojoji sun ceto mutane huɗu daga hannun ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da sojojin Najeriya suka yi. A yayin da ake ci gaba da gudanar da samame da nufin cafke fitaccen shugaban ‘yan fashin nan, Kachalla Muhammadu Fulani da ƙungiyar sa ta masu aikata laifuka.

Waɗanda aka ceto dai su ne Musa Yakuba mai shekaru 62 da Alhaji Sa’adu Dayi, mai shekaru 68 da Mukhtar Danja mai shekaru 36 sai Salisu Danja mai shekaru 50.

An kuɓutar da Waɗanda harin ya rutsa da su ne yayin da sojoji suka ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankunan da ‘yan ta’addan ke gudanar da ayyukansu.

Tuni ma’aikatan lafiya ta kai masu ɗauki sakamakon raunukan harbin bindiga da suka samu a lokacin da aka yi garkuwa da su.

Su waɗannan mutane da sojoji suka ceto sune aka gani a faifan bidiyo a yanar gizo tare da Manjo Janaral Rabe Abubakar mai ritaya kafin mutuwar sa.

By ukarofi