
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya tana aiki tuƙuru da na jihohi wajen ganin al’amuran ci-gaban sun bunƙasa tare da faɗaɗa damarmaki domin amfanin al’ummar Nijeriya.
Haka kuma, ya ce tana aikin tallafa wa masana’antu da ƙarfafa fannin tsaro musamman don ganin an daƙile ayyukan ta’addanci da suka addabi ƙasar na tsawon lokaci tare da tabbatar da ɗorewar samun nasarori a fannoni daban-daban na ƙasar.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Ado-Ekiti, Babban Birnin Jihar Ekiti a lokacin jaddada goyon bayan gwamnatin na sake zaɓar Gwamna Biodun Oyebanji na jam’iyyar APC a karo na biyu a zaɓen gwamnan jihar da za gudanar a ranar Asabar.
Da yake jawabi a madadin Shugaba Bola Tinubu, Shettima ya ce cigaba da zama gwamna a Ekiti na Oyebanji zuba jari ne a zaman lafiya, ci-gaba da kuma goben jihar.
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata su zaɓi Oyebanji da mataimakiyarsa Misis Monisade Afuye a zaɓen gwamnan da ke tafe domin cigaba da amfana da romon dimukraɗiyya.
A cewarsa, Gwamna Oyebanji ya nuna jajircewa da sadaukarwa akan walwalar al’ummar Ekiti wajen nuna tausayi, shugabanci da haƙuri, da sauraro bisa girmamawa, wanda hakan ya sa al’umma ke ƙaunar sa, saboda haka ya dace a sake ba shi dama ta biyu.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da dai sauransu, kamar yadda kakakin mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya bayyana a wata takarda.






